ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Cutar Sankarau Da Hanyoyin Magance Ta

by Sani Anwar
5 months ago
Sankarau

Kamar yadda aka sani ne, cutar Sankarau ta fi yaduwa a irin wannan lokaci na zafi, sannan kuma akwai abubuwa da dama da ke haddasa ta.

Masana ilimin kimiyya, sun kasa wannan kwayar cuta zuwa gida biyu; akwai Sankarau mai dauke da kwayar cutar Bakteriya, akwai kuma mai dauke da kwayar cutar Bairos.

Don haka, mai dauke da kwayar cutar Bairos; ita ce cutar Sankarau mafi hadari, domin kuwa; tana iya yin kisa nan take ko cikin kankanin lokaci, musamman idan ba a samu kulawar gaggawa ba. Kazalika, nau’ikan kwayoyin Bakteriyar da ke haddasa wannan cuta, na haifar da guba a cikin jini, sannan kuma su yada ta zuwa sassan jikin Dan’adam baki-daya.

ADVERTISEMENT

Sai kuma mai dauke da kwayar cutar Bairos, wadda ta fi yawa cikin nau’ikan cutar ta Sankarau, sai dai kuma, ita ce wadda ta fi rashin hatsari a cikinsu. Duk da cewa, tana sanya mutum cikin hali na rashin lafiya, amma ba ta cika yin kisa ba.

Har ila yau, ya kyautu a lura cewa; wannan cuta ta Sankarau, za ta iya kama kowa, duk da dai ta fi kama yara kanana. Sai dai, manyan mutane masu fama da cutar da kan shafi garkuwar jiki, kamar masu fama da cutar Kansa, na cikin hatsarin kamuwa da wannan cuta kwarai da gaske.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”

2 – 3 Cikin 10 Na Masu Cutar Diphtheria Na Iya Mutuwa A Katsina – NMA

Bugu da kari, kwayoyin cutar da ke haddasa cutar Sankarau na yaduwa ne daga mutum zuwa mutum, ta hanyar kusanci ko hada jiki ko kuma ta hanyar tari ko atishawa ko sumbata ko kuma cin abinci da cokali guda.

Haka zalika, wasu mutanen na iya yada cutar ba tare da sun san suna dauke da ita ba, akasarin mutanen da ke dauke da ita; ba su ma sani ba.

Matsalar a nan ita ce, wadanda ke dauke da cutar ba tare da sun sani ba, na iya yada ta ga sauran mutane; musamman masu rauni, kamar kananan yara da kuma tsofaffi.

Wannan dalili ne yasa yara dalibai, wadanda ke karatu a makarantu masu cunkoso ke saurin kamuwa tare da yada cutar cikin kankanin lokaci.

Alamomin Kamuwa Da Cutar Sankarau

Duk da cewa, akwai nau’ikan cutar Sankarau iri daban-daban, akwai kuwa wasu alamomin da za a iya lura da su ta hanyar gane cewa, mutum ya kamu da cutar kamar haka:

Zazzabi

Amai da gudawa

Ciwon kai mai tsanani

Rashin son haske

Taurin wuya

Dimaucewa

Fita daga hayyaci

Shidewa

Fitowar kuraje

Har ila yau, akwai kuma karin wasu alamomin da ya kamata a lura da su, musamman ga yara kanana kamar haka:

Rashin cin abinci

Kumburi mai tashi a kai

Rashin kuzari

Taurin jiki

Saboda haka, kamar yadda masana suka bayyana; da zarar an ga ire-iren wadannan alamomi, sai a hanzarta zuwa asibiti ba tare da wani bata lokaci ba. Sannan kuma, ba dole ne sai an jira an ga dukkanin wadannan alamomi da aka jero a sama ba, kafin a garzaya zuwa asibiti.

Hanyoyin Kare Kai Daga Wannan Cuta Ta Sankarau

Babbar hanyar kariya daga wannan cuta ta Sankarau ita ce, Rigakafi. Sanin kowa ne, gwamnatoci da dama na samar da Rigakafin Cutar Sanƙarau kyauta a asibitoci daban-daban, wadanda ake sakawa cikin jerin alluran rigakafi na wajibi lokaci zuwa lokaci.

Kazalika, sauran matakan kariya daga cutar sun hada da:

Tsafta

Bude tagogi

Kauce wa cunkoso a cikin dakuna da dai sauran makamantansu.

Saboda haka, jama’a ya zama wajibi a kula tare da sanya lura dangane da wannan cuta kwarai da gaske, musamman ganin yadda ta fi yin illa da tasiri a irin wannan lokaci na tsananin zafi.

Sankarau
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”
Manyan Labarai

Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”

September 3, 2026
Sankarau
Kiwon Lafiya

2 – 3 Cikin 10 Na Masu Cutar Diphtheria Na Iya Mutuwa A Katsina – NMA

August 30, 2026
Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
Kiwon Lafiya

Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?

August 29, 2026
Next Post
Bukatar Kyautata Alaka Tsakanin Surukai

Bukatar Kyautata Alaka Tsakanin Surukai

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.