ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bukatar Kyautata Alaka Tsakanin Surukai

by Rabi'at Sidi Bala
5 months ago
Alaka

Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma.

Tsokacinmu na yau zai yi duba game da yadda wasu surukan suke saka kafar wando daya da iyayen mijinsu, har su mayar da su tamkar kishiyoyinsu.

Dalilin hakan ya sa shafin TASKIRA jin ta bakin wasu daga cikin ma’abota shafin game da wannan batu; “Ko me yake janyo hakan?, Ta wacce hanya za a magance matsalar?”

ADVERTISEMENT

Ga dai bayanan nasu kamar haka:

Sunana Hassana Yahaya Iyayi daga Kano

LABARAI MASU NASABA

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?

Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?

Babban magana. Rashin tarbiyya ne ke jawo wa, dan kuwa Uwar’miji ai uwarka ce, tunda ta haifa maka mijin, indan akwai mutunci kuwa dole ka dauke ta uwa. Iskanci ne kawai da zallar fitsara. Dole shi mai gidan shi zai jajirce ya nuna mata uwarsa ita ce duniyarsa in taga za ta gyara to, in ba za ta gyara ba tayi waje. Ah to, su yi gaggawar gyarawa dan kuwa wata rana za su tsinci talatarsu a Laraba.

Sunana Aminu Adamu, Malam Madori, daga Jihar Jigawa:

To, magana ta gaskiya ita ce, da farko akwai rashin tarbiyya a wajen ita surukar da take takun saka da iyayen mijinta, na biyu kuma akwai rashin nuna girman iyayen ga dansu domin sai ya bada kofa matarsa za ta raina iyayensa. Hanyar farko mutum ya auro mace mai tarbiyya wadda ta san mutuncin iyayenta, to, za ta mutunta iyayenka. Na biyu kuma kai ma ka ke girmama iyayenta domin hakan zai taimaka wajen ita ma ta girmama naka. Shawarata a nan ita ce ya kamata mazaje  su rika nunawa matan da za su aura mutuncin iyayensu tun kafin su aure su, domin hakan zai taimaka su san matsayin iyayen ka, don haka dole su rike su hannu bibbiyu.

Sunana Fatima Nura Kila, Jihar Jigawa:

Akwai laifin matan, sannnan akwai na iyayen, wasu iyayen sukan hana dansu kyautatawa matarsa, wani abu na rayuwa wanda hakkinsa ne ya yi, daga nan sai su fara takun saka da matar. Wasu matan kuma tun daga waje kawaye sun gama hure mata kunne kan kar ta yadda a juya ta. Ta yadda za a magance dole ne iyayen mijin su rika daukar matar dansu a matsayin ‘yar su, ita kuma surukar ta dauke su a matsayin iyayenta. Yakamata mu matan, da iyayen mijin mu daina, domin hakan zai rika kawo samun sabani da yawa har akai ga auren ya mutu.

Sunana Anas Bin Malik Achilafiya, ‘Yankwashi daga Jihar Jigawa:

Wannan hali yawanci yana faruwa ne saboda rashin fahimtar juna, tsoron kada a kwace soyayyar miji, ko kuma tasirin maganganu daga waje da yake kara tayar da hankali. Haka kuma wani lokacin rashin hakuri, son nuna iko a gida, ko kuma rashin isasshen tarbiyya a kan yadda za a mu’amalanci iyayen miji na iya janyo wannan matsala. Maganin hakan shi ne a fara da gina fahimta da hakuri tsakanin suruka da iyayen miji, tare da tunawa da cewa su ma iyaye ne da ya kamata a girmama su. Miji ma yana da rawar takawa wajen sasanta su, ya nuna adalci da hikima domin kada a bar sabani ya girma.

Sunana Abubakar, Malam Madori daga Jihar Jigawa:

Saboda rashin fahimta ko jituwa, musamman inda za ka ga iyaye suna sanya ido akan abun da miji yake yi wa matarsa. Ita kuma uwa gudun tsoron rasa kulawar danta sai kishi da shaidan su yi tasiri a tsakanin su. A gaskiya, iyayen miji ba kishiyoyi ba ne, su iyaye ne da ya kamata a girmama. Haka kuma miji yana da rawar da zai taka wajen daidaita al’amura da saita iyaka cikin hikima. Abin da yake janyo hakan shi ne kishi da tsoron rasa kulawar miji, rashin fahimtar matsayin iyayen miji, tsoma bakin iyaye fiye da kima. Za a iya magance matsalar ta hanyar girmama juna da kuma kauda-kai ga abin da mazaje suke yi wa matayensu. Shawarata a nan ita ce, surukai su ji tsoron Allah su gyara halayensu, su koyi girmama iyayen miji kamar nasu iyayen.

Sunana Hafsat Sa’eed, daga Jihar Neja:

Su suke ja wa kansu, tunda mutum matar sa bata shiga sabgar suruka ba, amma suruka za ta shiga sabgar ta, ta saka mata ido. To, su kuma surukan dama na zamani ne ba kunya gare su ba. Ni dai a shawarce mutum idan yayi aure ya ajjiye uwarshi a gefe ka zauna da matarka kowa gidanshi daban. Kowa dai da irin yanayin shi, wani lokaci akan samu akasi daga iyayen miji, wani lokaci kuma daga ‘ya’yaye, babu wanda matsala bata faruwa daga gare shi.

Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Rano daga Jihar Kano:

Wasu rashin tarbiyya, wasu kuma surukanne suke kure hakurin yaran. Hanyoyin suna da yawa amma kadan daga ciki sune, dukka bangare biyun a rika duba da su wa za a hada alaka musamman ta aure, sannan kuma a rika duba gidan tarbiyya da kuma ilmin addini a dukka bangarorin ma’auratan. Shawarata a nan ita ce, gaskiya hakan ba tsari bane domin yaran kamata yayi su rika daukar surukansu a matsayin iyayensu tunda sune suka haifi mijin da suke aure, haka suma iyayen su rika daukar yaran a matsayin ‘ya’yansu na cikinsu, duba da farin cikin matansu tamkar farincikin yaran da suka haifa ne. Allah ya sa mu dace.

Sunana Comr, Nr.Ibrahim Lawan Stk:

Galibi hakan na faruwa ne sakamakon rashin fahimtar matsayin aure da iyali, hade da kishi da son a fi karkata gare su wajen mijin. A wasu lokuta kuma shisshigin kawayen banza ko wasu ‘yan’uwa na kara hura wutar rikicin, tare da rashin hakuri da girmamawa da kuma matsalar sadarwa tsakanin bangarorin biyu. Magance wannan matsala na bukatar a fara da gina fahimta da mutunta juna, sannan a rika tattaunawa cikin nutsuwa idan wata matsala ta taso maimakon rike ta a zuciya. Yana da muhimmanci miji ya tsaya a tsaka-tsaki cikin adalci, ba tare da nuna son kai ba, tare da kaucewa sauraron maganganun waje da kan jawo fitina. Shawara ga masu irin wannan dabi’a ita ce su gane cewa iyayen miji ba kishiya ba ne, iyaye ne da ya kamata a girmama su. Su yi hakuri, su kyautata mu’amala, su guji kishi mara amfani, domin zaman lafiya a gida yana kawo kwanciyar hankali da albarka a aure.

Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos, a Jihar Filato:

Wannan wani al’amari ne da ya dade yana kawo matsaloli a zamantakewar aure, a tsakanin al’ummomi daban-daban, tun tsawon shekaru. Irin wannan rigima tana iya kai wa ga raba kan maigida, da kuma shiga tsakanin sa da iyayensa ko ‘yan’uwan sa, ta hanyar kulla makirci ko asiri. Wani lokaci ma ‘yan’uwan mata ne ko iyayenta ke nuna takura ga mijin ‘yar su, da dora masa nauye-nauye ko rashin yarda da yadda zamantakewar auren su ke tafiya da ‘yarsu. A ganina, irin wannan zama na kishiyantar juna bai kamata ba, domin kowa matsayinsa daban, kuma babu wanda ya kamata ya nuna fifiko saboda an yi aure. Hakkin iyaye ne da ‘yan’uwan miji su ga ya zauna lafiya da iyalinsa, ita ma kuma hakkin iyayen mijinta ne ta girmama su kuma ta mutunta su, matukar tana son zama lafiya da dansu. Allah Ya ba mu fahimtar juna a tsakanin mu da iyalinmu da ‘yan’uwanmu.

Sunana Sadik Abubakar Abdullahi, Rijiyar Lemo, karamar hukumar Dala, Jihar Kano:

Wasu surukan kan dauki iyayen mazajensu tamkar kishiyoyi ne saboda rashin fahimtar matsayin iyaye ga rayuwar miji, da kuma kishi ko son mallakar kulawarsa gabadaya. Wani lokaci kuma rashin hakuri, rashin tarbiyya, ko zugar wasu mutane kan haddasa wannan dabi’a, har mace ta fara kallon duk wani kusanci tsakanin miji da iyayensa a matsayin barazana ga aurenta. Wannan tunani kuskure ne, domin iyaye suna da haki na musamman, kuma soyayyar da da yake yi musu ba ta rage kaunar da yake yi wa matarsa. Magance wannan matsala na bukatar fahimta, hakuri da girmama juna a tsakanin ma’aurata da iyayensu. Ya kamata mace ta gane cewa mutunta iyayen miji yana kara mata daraja, ba rage mata ta ba, shi kuma miji ya nuna adalci da hikima wajen tafiyar da dangantakarsa da matarsa da iyayensa.

Alaka
Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Yadda Alaƙata Da Adamu Zango Ta Bunƙasa A Kannywood —Jarumi Ibrahim Sodangi 
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim Ko Gaske:Yaushe Masu Kallon Fina-finai Za Su Daina Daukar Fim A Matsayin Gaske
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim ɗin ƙaddara: Anya Ana Samun Irin Wannan ƙaddarar Kuwa?
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?

MASU ALAKA

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?
Taskira

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?

September 5, 2026
Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?
Taskira

Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?

August 29, 2026
Tsakanin Digiri Da Sana’a Wanne Ya Fi Muhimmanci A Wannan Lokacin?
Taskira

Tsakanin Digiri Da Sana’a Wanne Ya Fi Muhimmanci A Wannan Lokacin?

July 25, 2026
Next Post
Tsohon Shugaban Croatia: Sin Tana Kallon Sauran Kasashe Daidai Da Juna

Tsohon Shugaban Croatia: Sin Tana Kallon Sauran Kasashe Daidai Da Juna

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.