Connect with us

LABARAI

Cutar Shan Inna Ta Barke A Jihohin Jigawa, Katsina Da Yobe

Published

on

Sakamakon tabbatar da sake barkewar cutar shan inna a Jihar Jigawa, Katsina da Yobe, gwamnatin Jihar Kano, ta shelanta fara aiwatar da allurar ta maganin na Polio, a kananan hukumomi tara na Jihar da suke kan iyaka da Jihohin da lamarin ya shafa.
A dukkanin kananan hukumomin da abin ya shafa, ana ci gaba da gudanar da allurar rigakafin a tsakankanin ranakun 1 zuwa 4 ga watanSatumba, 2018. Za a yi kashi na biyu a ranakun 22 da 25 ga watan na Disamba a dukkanin kananan hukumomin da suka hada kan iyaka da Jihar ta Jigawa domin hana yiwuwar yin safarar kwayan cutar zuwa cikin Jihar ta Kano.
Wannan shi ne yakin da hadakar kungiyar ‘yan jaridu masu yaki da cutar ta shan inna ta daura domin kawar da cutar ta Polio a dukkanin fadin Jihar, musamman a al’umman Makoda, Dambatta da Ajingi, domin tsarkake al’ummun daga cutar ta Polio.
A lokacin ziyartar da kungiyar ‘yan jaridun ta JAP ta kai, kimanin nisan kilomita 30 daga cikin birnin, Kwamishinan lafiya na Jihar, Dakta Kabiru Ibrahim Getso, wanda yake a garin na Makoda, ya yi wa jami’an lafiya na garin bayani, ya yi masu bayanin wajibcin su yi wa iyayen yaran yankin bayanan tilascin su kai ‘ya’yan su domin a yi masu allaurar rigakafin saboda sabuwar annoban da ta barke.
Getso ya bayyana kananan hukumomin da abin ya shafa kamar haka, Ajingi, Albasu, Dambatta, Gaya, Gabasawa Makoda, Minjibir, Kunchi, da Takai, wadanda duk sun hada kan iyaka da Jihar ta Jigawa.
Kwamishinan ya kuma yi amfani da wannan daman wajen nu na wa al’umman hanyoyin kare kai daga barkewar cutar a Jihar, wanda ya nu na masu cewa, hakan ba ya ratayu ne a kan gwamnati kadai ba, dukkanin masu ruwa da tsaki a Jihar, kamar su kungiyoyi, ‘yan jaridu, kungiyoyin al’ummu, iyaye da ma daidaiku duk suna da rawar da za su taka a kan hakan.
A nan kuma sai Getso ya karfafa bukatar al’umman da su rinka shan ruwa mai tsafta, ya ce masu, duk ruwan da suke da shakku a kansa su guje shi, ko kuma su tsarkake shi ta hanyar tafasawa da magani a ciki.
Advertisement

labarai