Ƙungiyar Likitocin Nijeriya (NARD) ta dakatar da yajin aikin da ta tsunduma na sai baba-ta-gani inda ta shafe kwanaki 29 bayan sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da Gwamnatin Tarayya, da nufin bayar da damar biyan buƙatun ƙungiyar da suka daɗe suna nema a wurin gwamnati.
Shugaban NARD, Dr. Mohammed Usman, ya sanar da wannan matakin a daren Asabar ta shafinsa na X, yana mai cewa Majalisar Zartarwa ta Ƙungiyar (NEC) ta yanke shawarar dakatar da “Yajin aikin gama gari, na sai baba-ta-gani” bayan shafe makonni huɗu don ba da damar aiwatar da muhimman yarjejeniyoyin da aka cimma.
- Yadda Gwamnatin Tarayya Da Wasu Jihohi Suka Rufe Makarantunsu Kan Matsalar Tsaro
- Fadar Shugaban Kasa Ta Karrama Daliban Da Suka Nuna Hazaka A 2025
Ya ce, dakatarwar ta biyo bayan jerin tarurrukan sulhu da aka yi da kuma wata sabuwar yarjejeniyar da aka sanya wa hannu tare da ke bayyana matsayin buƙatun ƙungiyar 19.
Ana sa ran likitoci a faɗin ƙasar za su dawo bakin aiki har zuwa lokacin da ƙungiyar ta yanke na ci gaba da yajin aiki idan aka gaza aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma.














