Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, na shirin gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika a gaban kuliya; Diyarsa Fatimah, da wasu mutane biyu a gaban kotu bisa zargin almundahana a gobe Alhamis, 9 ga watan Mayu, 2024.
Mutanen hudu na fuskantar tuhume-tuhume ne kan badakalar kwangilar Naira biliyan 2.7 da aka bankado a ma’aikatar sufurin jiragen sama karkashin jagorancin Sirika.
Za a gurfanar da tsohon Ministan ne a gaban kuliya a karon farko a gaban mai shari’a Sylvanus Oriji na babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Cikakken Labarai daga baya…