Shugaban hukumar Kidayar jama’a ta Nijeriya Nasir Isa Kwarra, ya ce ɗage zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin jihohi da ka yi a ƙasar ka iya shafar aikin ƙidayar jama’ar da aka shirya gudanarwa cikin watan Maris.
BBC Hausa ta rawaito cewa, Nasir din ya yi wannan iƙiƙari ne a lokacin da yake ganawa da wakilan asusun ƙidayar jama’a na Majalisar Dinkin Duniya a Abuja babban birnin ƙasar.
- NPC Ta Fara Horar Da Ma’aikata 786,741 Don Aikin Kidayar 2023
- Za A Fara Kidayar ‘Yan Nijeriya A Watan Maris – NPC
Hukumar zaɓen Nijeriya dai ta ɗage zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin jihohi da aka shirya gudanarwa ranar 11 ga watan Maris zuwa ranar 18 ga watan Maris.
shugaban hukumar ƙidayar ya shaida wa manema labarai cewa duk da kawo yanzu ba a saka tartibiyar ranar fara aikin ba, zai tuntuɓi shugaban ƙasar Muhammadu Buhari domin saka ranar da za a fara gudanar da wannan aiki.
A nata ɓangaren wakiliyar asusun Majalisar Dinkin Duniya kan ƙidayar jama’a Ms Ulla Mueller, ta alƙawarta bayar da tallafin asusun domin tabbatar da gudanar da aikin kamar yadda aka tsara.