Jam’iyyar PDP da ke mulki a jihar Bauchi ta sanar da cewa za ta sake gudanar da sabon zaben fitar da gwani na dan takararta da zai rike mata tutar neman kujerar gwamnan Jihar Bauchi a yayin babban zaben 2023 da ke tafe.
Sabon zaben zaben zai gudana a ranar Asabar kamar yadda wakilinmu ya nakalto daga uwar jam’iyyr a matakin jihar.
Sakataren watsa labarai na jam’iyyar PDP a jihar Bauchi, Alhaji Yayanuwa Zainabari, shi ne ya tabbatar da hakan ga wakilinmu a ranar Talata, ya bayyana cewar wannan matakin na zuwa ne biyo bayan janyewar radin kashin kai da Dan takarar da aka tsayar tun da farko Alhaji Kasim Ibrahim Muhammad ya yi na cewa bai da ra’ayin yin takarar kuma.
Ya ce, “Shi Kasim ya janye bisa radin kansa. Don haka jam’iyyar za ta gudanar da sabon zaben a ranar Asabar mai zuwa”.
Idan za ku iya tunawa dai gwamnan da ke kan kujerar Sanata Bala Muhammad ya nemi tikitin kujerar Shugaban kasa a jam’iyyar PDP amma ya fadi inda Atiku Abubakar ya kada shi da sauran ‘yan takara.
Wannan damar da jam’iyyar ta bayar tamkar yin alfarma ne ga gwamnan Jihar da ke ci a halin yanzu Bala Muhammad na ya sake samun damar neman kujerar gwamnan a karo na biyu.
Idan hakan ta tabbata, Bala Muhammad zai fafata neman kujerar gwamnan Jihar tare da tsohon Shugaban sojin saman Nijeriya, Air Marshal Sadiq Baba Abubakar da jam’iyyar APC ta tsayar a matsayin dan takararta.