Shugaban kasa Bola Tinubu, a ranar Talata ya gana da hafsoshin tsaro da sauran shugabannin hukumomin tsaro a fadar gwamnati da ke Abuja, kan karuwar rashin tsaro.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan ta’adda ke kara kaimi wajen kai hare-haren a wasu sassan kasar nan, musamman a babban birnin tarayya Abuja, inda masu garkuwa da mutane suka kai wasu hare-hare a cikin ‘yan kwanakin nan.
- A Kara Yawan Jami’an Tsaro A Hanyar Abuja- Kaduna – Sufeton ‘Yansanda
- Yadda Matsalar Tsaro Ta Addabi Al’ummomin Bwari A Abuja
Taron ya samu halartar babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Christopher Musa; Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja; Babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogala; Hafsan Hafsoshin Sojan Sama, Air Marshal Hassan Abubakar; Babban sufeto na ‘yansanda, Kayode Egbetokun, da sauran shugabannin hukumomin tsaro.
Duk da cewa ba a fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan taron, amma ana kyautata zaton cewa, shugaba Tinubu da hafsoshin tsaronsa za su yi nazari kan al’amuran tsaro a sassan kasar nan, inda za su ba da shawarwarin yadda za a shawo kan ‘yan ta’addan.