Gwamnatin jihar Borno ta rufe hedikwatar jam’iyyar NNPP ta Kwankwaso da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Hukumar raya birane ta jihar Borno ta rufe hedikwatar jam’iyyar tare da wasu ofisoshinta ne a ranar Alhamis.
Dan takarar gwamnan jihar Borno a karkashin jam’iyyar NNPP, Dakta Umaru Alkali, ya tabbatar da hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Maiduguri.
Ya ce “an kama dan takarar kujerar Sanata mai wakiltar mazabar Borno ta tsakiyar na jam’iyyar NNPP, Hon Attom Muhammad Maigira, bayan da ya amsa gayyatar ‘yansanda.
“An tura ‘yan sandan zuwa Sakatariyar Jam’iyyar da ke kusa da Abbaganaram da Gidan Maradara tsakanin Laraba zuwa Alhamis ne domin hana ‘yan jam’iyyar shiga ofishinsu.”
Wakilin Jaridar Daily trust da ya ziyarci mahadar Abbagannaram da misalin karfe 11:30 na safe, ya rahoto cewa, an girke ‘yan sandan kwantar da tarzoma da na fararen hula da motocin sintiri a harabar sakatariyar da aka kulle.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp