Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya amince da yi wa dukkan shugabannin hafsoshin tsaron Nijeriya da sufeto-Janar na ‘yan sanda da masu ba da shawara kan sha’anin tsaro da Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam murabus daga Ma’aikatunsu tare da maye gurbinsu nan take.
Hafsan hafsoshin sun hada da babban hafsan tsaro, Lucky Irabor da babban hafsan soji, Farouk Yahaya da Shugaban Hafsan Sojin Ruwa, Awwal Gambo sai shugaban hafsan sojin sama, Isiaka Amao da kuma Sufeto Janar na ‘Yansanda, Usman Alkali.
- Kungiya Ta Yaba Wa Shugaba Tinubu Kan Inganta Tsaro Da Yaki Da Rashawa
- Yanzu-yanzu: Tinubu Na Ganawa Ta Farko Da Shugabannin Tsaro
A cewar sanarwar da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya, sabbin jami’an da aka nada sune:
Mallam Nuhu Ribadu a matsayin babban mai ba da shawara kan sha’anin tsaron Nijeriya.
Sauran sun hada da “Maj. Janar C.G Musa Shugaban Hafsan Tsaro, Maj. T. A Lagbaja
“Shugaban hafson sojojin ruwa, Rear Admirral E. A Ogalla
“AVM H.B Abubakar Shugaban Hafsan Sojan Sama sai DIG Kayode Egbetokun Mukaddashin Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda.
“Maj. Janar EPA Undiandeye, matsayin shugaban hukumar leken asiri na kasa
Shugaban ya kuma amince da nadin:
“Col. Adebisi Onasanya, a matsayin kwamandan rundunar Soji.
“Lt. Col. Moshood Abiodun Yusuf, matsayin shugaban runduna ta 7, Asokoro, Abuja
“Lt. Col. Auwalu Baba Inuwa, matsayin shugaban runduna ta
177, Keffi, Nasarawa State
“Lt. Col. Mohammed J. Abdulkarim, matsayin shugaban runduna ta 102, Suleja, Niger
“Lt. Col. Olumide A. Akingbesote, matsayin shugaban runduna ta 176, Gwagwalada, Abuja
Kazalika, shugaban ya amince da nadin wasu hafsoshin soji a fadar shugaban kasa da suka hada da Maj. Isa Farouk Audu (N/14695) Babban Jami’i mai kula da Makamai na Gidan Gwamnati
“Capt. Kazeem Olalekan Sunmonu (N/16183) Babban Kwamandan Na Biyu
“Maj. Kamaru Koyejo Hamzat (N/14656) Babban Kwamandan Hukumar Leken Asiri ta Soja na fadar gwamnati
“Maj. TS Adeola (N/12860) Kwamanda, Makamai na Gidan Gwamnati
“Lt. A. Aminu (N/18578) Kwamandan Makamai na Gidan Gwamnati
Shugaban ya kuma amince da nadin wasu karin masu ba da shawara na musamman guda biyu (2), da manyan mataimaka biyu (2), wato:
“Hadiza Bala Usman mai ba da shawara ta musamman kan harkokin siyasa
“Hannatu Musa Musawa mai ba da shawara ta musamman kan tattalin arziki da al’adu
Sai Sanata Abdullahi Abubakar Gumel, matsayin mai ba da shawara kan sha’anin majalisar dokokin Nijeriya (Dattijai)
“Hon. (Barr) Olarewaju Kunle Ibrahim, matsayin babban mataimaki na musamman a majalisar wakilai ta Kasa (Majalisar Wakilai)
A karshe shugaban kasar ya amince da nadin Adeniyi Bashir Adewale a matsayin mai rikon mukamin Kwanturola Janar na Kwastam.
Sai dai shugabannin hukumar da aka nada da sufeto-janar na ‘yan sanda da kuma babban kwanturolan hukumar kwastam za su yi aiki a kan mukamansu, har sai an tabbatar da su kamar yadda kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya ya tanada.