ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?

by Muhammad Bakir Bello
3 days ago
Siyasa

Wannan makon ma, muna tare da kwararru kuma masana, masu fashin baki kan harkokin yau da kullum, wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu, kan shigar mata harkokin siyasa gadan-gadan. Kamar kowane mako, SANI ANWAR da MUHAMMAD BAKIR ne, suke tattaro ra’ayoyin.

Hajiya Medina Dauda Nadabo, daga Abuja.

A ra’ayina, ina goyon bayan shigar mata Siyasa gadan-gadan, saboda an fi samun masu gudanar da mulki da gaskiya da adalci a cikin mata.

ADVERTISEMENT

Allah ya yi mata da hakuri da kuma tausayi. Mata rabin al’umma ne, idan za mu yi magana a kan ilimi, kiwon lafiya, harkar kasuwanci da samar da ruwan sha, wadannan abubuwa ne da suka fi shafar mata da yara. Don haka, dole sai an samu mata a teburin da ake yanke hukunci, domin su fito da matsalar da suke fuskanta, don a magance su.

Sannan kuma, mata suna da salo na sulhu da gudanarwa, alal misali, a gidaje, a kasuwa, ko a makarantu, mata sun san yadda ake magance rigima da hada kai. Saboda haka, ana bukatar irin wannan kwarewa a majalisa da gwamnati.

LABARAI MASU NASABA

Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?

Tsakanin Digiri Da Sana’a Wanne Ya Fi Muhimmanci A Wannan Lokacin?

Har ila yau, Nijeriya na bukatar sautin da ke kawo sulhu, ba rikici kawai ba. Misali, ga ‘ya’ya mata, idan yarinya ta ga mace ta zama Sanata ko Gwamna ko Shugaba a wata ma’aikata mai girma, hakan zai sa ta yi begen cewa; “ita ma za ta iya”. Wannan yana kara karfin gwiwa ga wadanda ke da kwazo.

Wani abin dubawa shi ne, kalubalen rikicin siyasa da batun kudi da kuma al’ada, sukan hana mata shiga siyasa. Amma hakan bai kamata ya hana su ba, ya kamata mu gyara tsarin domin bai wa mata dama.

Addini ma bai hana ilimi da hidimar al’umma ba. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasalaam, ya bai wa mata dama su bayar da shawara. Don haka, siyasa ma wani bangare ne na irin wannan hidima.

A takaice, Nijeriya ba za ta ci gaba da kyau ba, sai an hada karfi da kokarin maza da na mata a siyasa.

Mairo Muhammad Mudi, daga Suleja Jihar Neja

A ganina, shigar mata siyasa gadan-gadan, abu ne mai matukar muhimmanci, domin mata bai kamata su kasance masu kada kuri’a kadai ba; ya kamata su kasance cikin masu yanke shawara.

Mata suna da kwarewa, basira da fahimtar matsalolin iyalai da al’umma. Don haka, kasancewarsu a majalisa da wuraren yanke hukunci, na iya taimakawa wajen samar da manufofin da suka fi shafar rayuwar jama’a.

Amma shigar mata siyasa bai kamata ya zama kawai neman mukami ba. Ya kamata mace ta shiga siyasa da manufa, ilimi, kishin kasa da kuma tsayawa kan gaskiya. Haka kuma, bai kamata a tilasta musu yin siyasa ta hanyar kwaikwayon munanan halayen da wasu suka saba da su ba. Za ta iya kasancewa mai karfi a siyasa tare da kiyaye mutuncinta, kimarta da ka’idojinta.

Abin da ya fi muhimmanci shi ne, a samar wa mata damar shiga siyasa cikin adalci, ba tare da nuna musu wariya ko amfani da su a matsayin kayan ado na jam’iyya ba. Idan aka ba su dama ta gaskiya, aka horar da su kuma aka saurari muryoyinsu, mata za su iya zama babbar hanyar kawo ci gaba da kyakkyawan shugabanci a Nijeriya.

Fadilah Isma’il (Fapus), daga Abuja

Ra’ayi na shi ne, ya kamata a bai wa mata dama domin su ma su taka tasu rawar a fagen siyasa. A koda-yaushe, a kan yi kazafi kancewa; mata na da rauni. Saboda haka, ba za su iya rike manyan mukamai ba. Amma kuma ya kamata mu san cewa, tun zamanin Annabawa ake da jaruman mata, kamar irin su Ummul Salama, wacce take bai wa Annabinmu shawarwari a kan siyasa da zamantakewar rayuwa.

Haka nan, idan aka yi la’akari da Nana Fatima da mahaiyifarta, Nana Khadija, za a fahimci irin rawar da mata suke takawa idan an ba su dama da kuma sarari na baza ilimisu.

Bugu da kari, har a wannan a wannan zamani da muke cik, da zarar ka samu matan da suka yi fice a sha’anin siyasa, za ka same su da gaskiya da rikon amana. Saboda a koda-yaushe, ita ‘ya mace mai son kurewa ruwa gudu ce. Idan za ta yi abu, ta kan so ta yi shi yadda ya kamata, ta yadda wani namijin ba zai iya kushewa ba.

Matan da suka yi fice a fannin siyasa, irin su Dakta Mariya Mahmoud Bunkure, Hannatu Musawa, Imaan sulaiman, Aisha Dahiru (Binani) da Hadiza Balarabe, dukkanninsu ba kanwar lasa ba ne wurin nuna jarumta da kwazo a hukumomin da suke shugabanta.

Don haka, ya kamata a bai wa mata dama fiye da damar da suke da ita a fannin wakilta da shugabanci, domin samun damar nuna baiwa da kwarewar da suke da ita.

Hasan Mansur, daga Zariya Jihar Kaduna

Ina goyon bayan bai wa mata dama a fagen siyasa dari bisa dari. Siyasa ba ta maza kadai ce ba. Dalili kuwa, wasu matan da dama sun fi maza ilimi da wayewa.

Har ila yau, wasu matan sun fi maza iya jagoranci. Matsalarmu a nan ita ce, ba a ba su damar da za su shigo a dama da su. Ina da yakinin cewa, idan aka ba su kujerar mulki, ba wai za su dauke ta a matsayin ado ba ne, illa yin abin da ya kamata.

Ali Isa Waziri

Ya kamata su ma mata su shiga harkokin siyasa a rika damawa da su. Dalili kuwa, duk abin da aka yi yana shafar su, sannan kuma akwai rawar da za su iya takawa, wanda mazan ma ba za su iya ba, saboda mata suna da tasiri sosai a aikin al’umma.

Amina Bello, Jihar Kaduna

A ra’ayina, babu laifi idan mace ta shiga siyasa gadan-gadan, muddin za ta iya kiyaye iyakokin addini da na al’adunmu. Mata suna da rawar da za su iya takawa, wajen kawo sauyi, musamman a fannin ilimi da lafiyar mata, amma sai ta tabbatar ba za ta yi wani abu da zai iya bata mata mutunci ba. Idan za ta yi, ta ji tsoron Allah, ta kuma yi adalci.

Mahadi Isa Waziri , daga Jihar Kano

Eh to! A ra’ayina, mata suna da muhimmiyar rawar da za su iya takawa a fagen siyasa, kuma kamar kowane dan kasa, suna da ‘yancin shiga siyasa.

Saboda haka, ina goyon bayan mata su shiga siyasa, amma kuma su yi ta a tsaftace, kuma cikin kamun kai da sanin mutuncin kansu.

Abdulrahman Umar Koko

Ina da ra’ayin mata su shiga siyasa gadan-gadan, domin kuwa an yi matukar barin su a baya. Kusan maza ne suka mamaye harkokin siyasar wannan kasa, duk da cewa; sanin kowa ne, mata sun fi kowa fitowa a fafata da su a lokutan zabe.

Don haka, idan aka yi la’akari da irin matsi da wahalhalun da mata suke sha a wannan kasa, ya kamata su ma su samu wakilci a dukkanin fannoni da sauran mukaman da ake da su.

Siyasa
Muhammad Bakir Bello
+ postsBio
    This author does not have any more posts.

MASU ALAKA

Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?
Taskira

Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?

August 29, 2026
Tsakanin Digiri Da Sana’a Wanne Ya Fi Muhimmanci A Wannan Lokacin?
Taskira

Tsakanin Digiri Da Sana’a Wanne Ya Fi Muhimmanci A Wannan Lokacin?

July 25, 2026
Tasirin AI (Artificial Intelligence) A Harkokin Al’umma Na Yau Da Kullum
Taskira

Tasirin AI (Artificial Intelligence) A Harkokin Al’umma Na Yau Da Kullum

July 18, 2026
Next Post
Siyasa

Ya Kamata EFCC Ta Sake Buɗe Fayal Ɗin Atiku - Tsohon Dan Majalisa

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026
Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.