ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsakanin Talauci Da Jahilci Wanne Ya Fi Jefa Matasa Mummunar Hanya?

by Rabi'at Sidi Bala
3 weeks ago
Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Mahawararmu ta wannan makon, ta kunshi jin ra’ayoyin masu karatunmu ne, kan jin shin tsakanin talauci da jahilci, wanne ya fi jefa matasanmu cikin mummunar hanya? Kamar kowane mako, SANI ANWAR da MUHAMMAD BAkIR, ne suka tattara ra’ayoyin naku.

Nana Aishatu Kabir Ladan

Talauci

Jahilci ba wai kawai rashin zuwa makaranta ba ne, ya hada har da rashin fahimtar abin da ya dace, da wanda bai dace ba, da kuma rashin sanin illar wasu shawarwari. Hakan kan sa matashi ya kasa bambance nagartaccen abu da akasin haka, ya zama mai saukin yaudara, ya bi mugayen mutane ko ya shiga ayyukan da bai fahimci illarsu ba. Wasu kuma kan dauki abin da ke cutar da rayuwarsu a matsayin abin alfahari ko hanyar samun nasara.

ADVERTISEMENT

Saboda haka, ina kira ga iyaye, malamai, gwamnati da sauran al’umma baki-daya, da su bai wa ilimin matasa muhimmiyar kulawa. Domin idan muka ilmantar da matashi daya ko biyu, muna daukar mataki ne wajen gina al’umma baki-daya, domin matasa su ne kashin bayan ci gaban kowace al’umma.

Safiyya Aminu Ibrahim

LABARAI MASU NASABA

Da Kazantar Muhalli Da Ta Jiki, Wacce Ta Fi Cutarwa

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?

Talauci

Talauci yana sa matashi ya ji cewa, dole sai ya samu kudi ko ta halin kaka, daga nan sai wasu su shiga aikata sace-sace, danfara, shaye-shaye da sauran makamantansu. 

Har ila yau, talauci yana sa mutum ya gaggauta yanke hukunci ba tare da yin nazari ko tunani ba. 

Amma akwai matasa talakawa da yawa, wadanda ba sa shiga mummunar hanya, suna kuma hakura su yi sana’a da karatu, saboda suna da ilimi da tarbiyya a zuciyarsu.

Fateemah Sadeek Ahmad

Talauci

Jahilci ko rashin ilimi, na iya hana matashi samun ilimin da zai taimaka masa wajen bambance tsakanin halal da haram. Gane hadarin wasu hanyoyi ko samun sana’ar dogaro da kai na nuna cewa; rashin samun ingantaccen ilimi da kwarewa na daga cikin manyan kalubalen matasa a Nijeriya.

Bashir Sabo Nadabo (Baban Yazdan)

Talauci

A gaskiya, ni ina ganin talauci ya fi jahilci muni. Domin idan mutum yana da ilimi, ko da talauci ya matsa masa, iliminsa na iya taimaka masa wajen sanin abin da ya dace da wanda bai dace ba, ya kuma nemo mafita ta halal. Amma idan talauci ya hadu da jahilci, matsalar kan kara tsanani; mutum na iya fadawa cikin sata, garkuwa da mutane da sauran munanan ayyuka, saboda matsin rayuwa da rashin ilimin da zai taimaka masa ya samu mafita.
Haka kuma, jahilci shi kadai ma wata babbar matsala ce, domin mutum na iya kasa fahimtar gaskiya ko da an yi masa nasiha. Saboda haka, a ganina talauci da jahilci dukkansu suna da hadari, amma haduwarsu ita ce mafi muni. Ai ko Uban Giji ma ya ce; “Mugun ciwo talauci.”

A ganina, jahilci ya fi jefa matasa cikin mummunar hanya. Domin kuwa, yana iya sanya mutum cikin wahala, amma idan matashi yana da ilimi da fahimtar rayuwa, zai iya nemo wa kansa hanya ko mafita daga talauci ta hanyar yin aiki, sana’a ko neman ilimi.

Jahilci kuwa, yana hana mutum sanin abin da yake yi na daidai da abin da ba na daidai ba. Matashi marar ilimi da tarbiyya, zai iya fadawa cikin miyagun dabi’u, kamar shaye-shaye, sata, daba da sauran miyagun laifuka, musamman ma idan abokansa suna rinjayar sa.

Haka kuma, ilimi yana taimaka wa matashi wajen fahimtar muhimmancin aiki, hakuri da bin doka. Duk da cewa, talauci babbar matsala ce, amma jahilci kuma na iya sa mutum ya kasa gane hanyar da za ta fitar da shi daga talauci.

A karshe, ya kamata a bai wa matasa ilimi mai inganci da tarbiyya, tare da samar musu da ayyukan yi, domin zama masu dogaro da kawunansu da kuma amfani ga sauran al’umma baki-daya.

Muhammad Sani 

Talauci

 Idan muka yi nazarin al’amura da hankali, jahilci ya fi hadari.
Amma kuma, talauci yana iya zama babban kalubale mai tsanani. Yunwa da rashin dama suna iya tura matashi zuwa ga aikata sata, karya da sauran miyagun laifuka. Amma kuma, talauci ba shi da karfin jefa mutum cikin mummunar rayuwa kamar yadda ake zato. Domin kuwa, mutumin da yake da ilimi da wayewa yana iya fuskantar talauci da kwazo da hankali, kuma yana iya gina hanyarsa ta fita daga ciki.

Jahilci kuwa, yana da wani karfi na musamman, don kuwa yana makantar da hankali tare da hana mutum gane sakamakon ayyukansa. Matashin da ba shi da dabara, kuma bai san yadda ake gina rayuwa mai dorewa ba, yana iya shiga shari’a cikin sauki. Haka kuma, jahilci shi ne yake sa talauci ya dore. Duk mutumin da ya samu ilimi, yana iya fita daga talauci; amma mutumin da yake da kudi, amma ya kasance jahili, yana iya rasa duk abin da yake da shi.

Don haka, idan muka auna biyun, jahilci ya fi jefa matasa cikin mummunar hanya. Talauci kalubale ne; jahilci kuwa hanya ce ta rushewa. Matasan da ke da ilimi, suna da damar gina rayuwarsu komai wuya; amma matasan da ke da jahilci, suna da damar rasa rayuwarsu duk wadatarsu.

Ahmad Bello Hamza 

Talauci

A ganina, jahilci ya fi talauci jefa matasa cikin mummunar hanya, saboda rashin ilimi da wayewa na iya sa matashi ya kasa gane bambancin abin da ya dace da wanda bai dace ba. Jahilci na iya hana shi fahimtar damar da ke gabansa, ya kuma sa ya zama mai saukin tasiri daga abokai ko wasu mutane.

Talauci kuwa, yana iya tilasta matashi fuskantar matsaloli, amma ilimi da wayewa na iya taimaka masa wajen nemo hanyar fita daga wannan hali. Saboda haka, yaki da jahilci yana daga cikin muhimman hanyoyin kare matasa daga shiga mummunar hanya.

Mahadi Isa Waziri 

Talauci

Jahilci, saboda shi ne yake sa mutum yayi abu ba tare da tunanin me zai je ya zo ba. Idan mutum yana da ilimi, kuma yana aiki da shi, rashin abin hannu ko talauci ba zai sa ya yi abin da bai kamata ba. 

Yana da wahala ka ga abin mai ilimin da yake aiki da shi ya shiga wani hali na aikata abin da bai dace ba, saboda talauci. Ta yiwu za a iya samu, amma ‘yan kalilan ne. 

Yusuf Usama Muhammad 

Talauci

A gaskiya jahilci ya fi jefa matasa cikin mummunan hali, kai ba ma matasa kadai ba, har da sauran al’umma baki-daya. Idan ka duba, yanzu mafi akasarin matsololin da muke fama da su, ummul aba isin su shi ne jahilci, kamar su shaye-shaye, daba, bangar siyasa, fyade, ‘yan bindiga da dai sauransu, wanda da a ce akwai ilimi, da abubuwa da dama ba za su yi muni haka ba, hatta shi kansa talauci, idan akwai ilimi ba zai yi kamari. Saboda haka, ilimi shi ne rayuwa da kuma mafita a dukkanin bangarori, kamar zamantakewa, addini, kasuwanci da sauran makamantansu.

Talauci
Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Da Kazantar Muhalli Da Ta Jiki, Wacce Ta Fi Cutarwa
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Yadda Alaƙata Da Adamu Zango Ta Bunƙasa A Kannywood —Jarumi Ibrahim Sodangi 
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim Ko Gaske:Yaushe Masu Kallon Fina-finai Za Su Daina Daukar Fim A Matsayin Gaske
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim ɗin ƙaddara: Anya Ana Samun Irin Wannan ƙaddarar Kuwa?

MASU ALAKA

Da Kazantar Muhalli Da Ta Jiki, Wacce Ta Fi Cutarwa
Taskira

Da Kazantar Muhalli Da Ta Jiki, Wacce Ta Fi Cutarwa

October 11, 2026
Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?
Taskira

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?

September 5, 2026
Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?
Taskira

Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?

August 29, 2026
Next Post
Har Yanzun Ba A Kawo Ƙarshen Boko Haram Ba, Kawai Dai An Raunana Su – Gwamna Inuwa 

Har Yanzun Ba A Kawo Ƙarshen Boko Haram Ba, Kawai Dai An Raunana Su - Gwamna Inuwa 

LABARAI MASU NASABA

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026

Shugabar Jaridar LEADERSHIP Ta Halarci Bikin Aza Harsashin Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙire Tare Da Remi Tinubu A Abuja

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

October 23, 2026
Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

October 23, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

October 23, 2026
Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

October 23, 2026
Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

October 23, 2026
Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’

Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.