Shiyyar Kudu Maso Yammacin kasar nan ka iya samun karin jihohi uku muddin majalisar wakilai ta amince da bukatar da ke gabanta.
Kudurin wanda dan majalisar da ke wakiltar mazabar bokun/Oriade daga Jihar Osun, Hon Oluwole Oke ya gabatar.
- Zargin Badakala: Emifiele Ya Sake Shiga Tsaka Mai Wuya Kan Dala Miliyan 6
- Wata Mata Ta Taba Zagina A Kan Littafina ‘Umarnin Uba’ —Yareema Shaheed
A cikin bukatar da ke kunshe cikin kudurin shi ne, domin a kara wasu jihohi masu suna Oke-Ogun, Ijebu da Ife-Ijesa.
A cewar kudurin dokar, Jihar Oke-Ogun za ta kasance tana da babban birninta Iseyin, kuma ta kunshi kananan hukumomi 12 ne da suka hada da Olorunsogo, Irepo, Oorerelope, Ogbomosho ta arewa, Ogbomosho ta kudu, Saki ta gabas, Saki ta yamma, Atisbo, Itesiwaju, Iwajowa, Kajola da kuma Iseyin.
Jihar Ijebu, muddin aka amince da kafata, za ta kunshi kananan hukumomin Ijebu ta gabas, Ijebu ta arewa masa gabas, Ijebu Ode, Ikenne, Odogbolu, Ogun Waterside, Remo ta arewa da Sagamu. Sannan, an tsara cewa babban birnin Jihar Ijebu zai kasance Ijebu Ode ne.
Yayin da ita kuma Jihar Ife Ijesa za ta tattaro kananan hukumomi 11 ta hadesu wuri guda ta kasance musu jiha, wadannan kananan hukumomin sun hada da Atakunmosa ta gabas, Atakunmosa ta yamma, Boluwaduro, Ife ta tsakiya, Ife ta gabas, Ife ta arewa, Ife ta kudu, Ilesa ta gabas, Ilesa ta yamma, Oboku da kuma Oriade.
A wata wasika kai tsaye da aka aika ga akawun majalisar, mai dauke da kwanan wata 6 ga watan Fabrairun 2024, Oke na cewa, “Ina farin cikin aiko maka da wannan kudirin domin daukan matakan da suka dace na gabatar da shi a gaban zauren majalisa.”
Shiyyar Kudu Maso Yammacin Nijeriya dai a halin yanzu na dauke da jihohi ne guda shida, da suka hada da Ondo, Oyo, Legas, Ogun, Osun da kuma Ekiti.