A daidai lokacin da al’umma ke alhinin kisan da ‘yan ta’adda suka yi wa Mai Martaba Sarkin Gobir, Isa Bawa, bayan da suka yi garkuwa da shi a dajin Sakkwato, jami’an tsaro sun dukufa wajen ganin sun cafko ‘yan ta’addan da suka aikata wannan ta’asar.
Domin samun cikakken nasara a faufukar kamo wadanna ‘yan ta’addan tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Ibrahim Ali Pantami ya bayar da shawarwarin dabarun da ya kamata jami’a tsaronmu su yi amfani da su domin cafko ‘yan ta’addan a cikin sauki.
- Mun Dakile Yunkurin Kutse Ta Intanet Har Sau Miliyan 12 Lokacin Zabe – Pantami
- AU Ta Naɗa Pantami Shugaban Tsara Manufofin Masana’antun Afrika Karo Na 4
A wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sadarwa, Farfesa Pantami ya ce, za a iya kama wadannan ‘yan ta’adda a cikin sauki ta hanyar amfani nambobin SIM da NIN rajista da aka yi wa duk wani layin waya da ake amfani da shi.
Ya ce, a lokacin yana minista ya tabbatar da fara aiki da Sim da NIN Registration wanda in har an bi diddigi to babu wani barna da za a yi a fadin kasar nan da ba za a iya gano wanda ya aikata ba da kuma inda aka aikata ba. “Mun sha rubuta takarda a kan haka ga jami’an tsaro muna sanar dasu hanyoyin amfani da wannan dabarun, Allah ne shaida” in ji shi.
Ya ce, zuwa lokacin da ya sauka a kan karagar minista ya bar mutum fiye da miliyan 100 masu rajistar SIM da NIN kuma a lokacinsa ne aka yi wa mutum miliyan 60 rajistar. “Manufar shi ne don a samar wa da masu tsaro wani dandamali da za su yi amfani da shi wajen cimma manufar da ake bukata.
Ya kuma bayyana cewa, an sha yi masa barazana ga rayuwarsa a kan yadda ya tsayu na sai an yi amfani da tsarin yi wa Sim da NIN rajista.
Masana na ganin lallai ya kamata jami’an tsaro su rungumi wannan shawarar na Farfesa Pantami don a kawo karshen ayyukan ta’addanci a Nijeriya.
Idan za a iya tunawa a makon jiya ne al’umma sun kadu game da labarin kisan da ‘dan bindiga suka yi wa Sarkin Gobir na Gatawa Isa Bawa, bayan kwashe makwanni a hannun dan bindiga.
Lamarin ya zo ne kimanin mako daya bayan sakin wani bidiyo da ya rika yawo a shafukan sada zumunta, wanda ya nuna sarkin a hannun masu garkuwa da shi yana rokon gwamnati da iyalansa su cece shi daga hannun ‘dan bindiga.
Duk da cewa dan bindigar sun kwashe shekaru suna kashe-kashe a yankin na arewacin Najeriya, amma ba kasafai ake samun irin haka ba.
Sai dai sau da yawa bayan an gama jimami, lamarin sai ya kwanta sai kuma idan wani lamarin makamancin haka ya sake faruwa a gaba.
Gwamnatin Nijeriya dai ta dade tana cewa tana bakin kokarinta wajen shawo kan matsalar ta dan fashin daji, to amma abin na ci gaba da addabar al’ummar jihohi da dama.
Su ma gwamnonin jihohin na iyakar bakin kokarinsu ta wani fannin.
Tuni gwamnatocin jihohin yankin irin su Katsina da Zamfara da ita kanta Sokoto suka kaddamar da rundunonin dan sa-kai na jihohi domin shawo kan matsalar, amma har yanzu babu jihar da aka kawar da matsalar baki daya.