Abdulkadir Abubakar, wani matashi ne mai jini a jika da ya kasance mai sanyin hali da sanin ya kamata wanda ya kammala Digirinsa na farko a Jami’ar Alqalam da ke Jihar Katsina a fannin kiwon lafiya.
Ya kasance abin so a cikin dangi saboda yadda yake da biyayya da haƙuri da kuma girmama na gaba da shi.
Sai dai kash! Ashe Allah bai yi shi mai tsawon kwana ba yayin da ya gamu da ajalinsa lokacin da yake ƙoƙarin taimakawa wajen ganin ‘yan bindiga sun sako wasu ‘yan uwansa maza da mata da aka yi garkuwa da su.
- Hajjin Bana: Muna Alfahari Da Goyon Bayan Gwamnan Kaduna– Abubakar Yusuf
- Jirgin Ƙasan Kaduna Zuwa Kano Zai Fara Aiki Farkon 2025
Majiyarmu ta shaida mana cewa, wasu ‘yan bindiga sun yi dirar mikiya a wata ruga da ke wajen garin Jere a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, inda suka yi awon gaba da wasu magidanta da iyalansu zuwa dajin Kachiya da ke Kudancin Kaduna.
Saboda yadda aka yi amanna da sanyin halin ran Abdulkadir Abubakar wanda aka fi sani da Abba, sai aka nemi ya tattauna da ‘yan bindigar domin samun maslaha a kan yadda za a sako su.
Bayan ya tattauna da su an cimma matsaya, ana kamar babbar sallah saura sati uku, Abba tare da wasu mutum biyu suka tafi yankin Kachiya domin kai kuɗin fansa.
Majiyarmu wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta ci gaba da cewa, “ana gobe za su tafi, a lokacin da Abba ya shiga wurin mahaifiyarsa don su yi sallama, ta ce masa, anya Abba!
Ko za ka haƙura da kai kuɗin fansar nan, ka bari wasu su kai, Abba ya ce mata Baba kar ki damu in sha Allahu babu abin da zai faru.
Ni idan na je ma zan tsaya a wurin mota ba zan shiga dajin ba. Ai kuwa ashe sallamar ƙarshe za su yi.
“Washe gari bayan sun isa wurin da ‘yan bindigar suka ce a kai kuɗin, sai suka tsaya, ‘yan bindigar suka kira waya suka ce Abba za a ba kuɗin ya kawo musu cikin daji.
“Abokan tafiyarsa suka ce Abba kar ka je, ya ce musu babu komai tun da ni suke so na kai musu kuɗin bari na je, sai ga wani mai mashin ya fito daga daji, suka ce masa ya hau.
“Ya hau sun fara tafiya kaɗan sai ga wani kuma ya sake fitowa daga daji ya hau baya suka sa Abba a tsakiya.
“To, baya sun isa can sai ‘yan bindigar suka sako mutum ɗaya daga cikin mutanen da suka sace. Aka tambayi wanda suka sako sai ya ce ai sun riƙe Abba.
“Haka aka dawo, wallahi duk jikinmu ya yi sanyi, ga shi ba su sako wadancan ba kuma sun riƙe Abba.”
Majiyar ta ƙara da cewa, bayan kudin fansar da aka kai musu fiye da Naura miliyan 10, sai suka ce a sake kai musu miliyan uku da babura huɗu sai su sako sauran mutanen tare da Abba.
“Washe garin sallah, an yi waya da su har suka ce a zo wa Abba da kaya masu kyau ya sa saboda na jikinsa duk sun lalace. Aka sake ɗaukar kudin aka kai musu. Waɗanda suka kai kudin sun jira su tun daga hantsi har zuwa la’asar ba su ga kowa ba, su kuma suna jin tsoron kar dare ya yi musu a daji sai suka dawo.
“Ana ganin motarsu ta dawo aka tarbe su da murna ana ga Abba ya dawo, ga Abba ya dawo. Sai da aka buɗe mota aka ga shiru babu Abba. Tun daga nan jikinmu ya ƙara sanyi, muka shiga fargaba.
“To, bayan sun sake kiran waya washegari shi ne suka ce a sake kawo musu kudi ko kuma su ma sauran su kashe su. Daga nan muka tabbatar da cewa lallai sun kashe Abba.
“Ashe ma sun riga sun kashe shi tun fiye da kwana 10 da suka wuce kuma suka jefa gawarsa a ruwa.
“Yanzu haka ma an riga an yi wa Abba salatul ga’ib wanda ake yi wa mutumin da ya mutu amma babu gawarsa a kusa. Wallahi muna cikin tashin hankali, ” in ji majiyar tamu.
Duk ƙoƙarin da muka yi don jin ta bakin jami’an tsaro dai abin ya faskara amma muna ci gaba da bibiyar Jami’in hulda da jama’a na Rundunar ‘Yansandan Kaduna.