Shahararren mawakin da wakokinsa ke haskawa a yanzu ABBA SHAFI’U UMAR Wanda aka fi sani da ABBA GANGA ya bayyana wa masu karatu dalilin da ya sa ya fara yin waka, ya kuma bayyana irin nasarorin da ya samu game da waka, har ma da wasu batutuwan da suka shafi sana’arsa ta waka ga dai tattaunawa tare da wakilinmu YAKUBU FURODUSA GWAMMAJA kamar haka:
Masu karatu za su so su ji cikakken sunanka tare da dan takaitaccen tarihinka
- Wike Ga Atiku : Kar Ka Zarge Ni In Ka Fadi A Zabe
- Rashin Shugabaci Nagari Ya Jefa Nijeriya Halin Da Take Ciki, In Ji SDP
Sunana Abba Shafi’u Umar wanda aka fi sani da Abba Ganga. An haife ni a unguwar Gwammaja Makafin Dala Jihar Kano na yi karatun firamare a ‘Dala Special Primary School’ na yi karatun Sakandare a gwammaja 1.
Me ya ja hankalinka har ka tsunduma harkar waka?
Gaskiya abin da ya ja hankalina na fara sana’ar waka ba komai ba ne face fadawa soyayya da na yi ta wata yarinya daga baya kuma da na ga nima ina da gudunmawar da zan bayar sai na tsunduma harkar ka in da na in.
Za ka yi kamar shekara nawa kana waka?
Shekara goma yanzu haka cikin harkar waka.
Nawa ne adadin wakokin da ka yi?
Na yi wakoki da yawa amma iya na soyayya sun kai hamsin. Da wacce waka ka fara? Wakar siyasa ce da na yi wa wani dan takarar gwamna.
Ya karbuwar wakar ta kasance a wajen jama’a?
Gaskiya wakar ta karbu sosai saboda shi kansa gwamnan ya yi mamakin abubuwan dana fada a wakar kuma gani yaro karami.
A gaba daya wakokin da ka yi idan aka ce ka fidda bakandamiyarka wacce ka fi so, wacce za ka ce?
Gaskiya wakar dana fi so ita ce wakata ta ‘Arashi’ na so wakar da Garzali Miko da Maryam Yahaya suka hau saboda a ita ce mutane suka fara gane ni.
Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance?
Eh gaskiya na yi gwagwarmaya sosai kuma na tsaya na yi aiki tukuru.
Ko akwai wani kalubale da ka taba fuskanta game da waka?
Eh! gaskiya na samu kalubale a lokacin dana fara daga gida amma yanzu alhmadullah komai ya wuce.
Toh ya batun Nasarori fa?
Na samu nasarori da yawa na farko alhamdullah na yi wakokin da aka ji su a duniya sannan na samu kyaututtuka na award a ciki kuma har da kyautar mota.
Wanne abu ne ya taba faruwa da kai na farin ciki ko akasin haka?
Abin da ya faru dani na bakin ciki gaskiya na manta saboda ban cika rike irin wannan ba amma abin da ya faru dani na farin ciki shi ne idan wata kyauta da aka yi min dalilin waka.
Wane ne babban abokinka a mawaka?
Eh gaskiya babban abokina a wannan harka shi ne makidina Asim Labbaika.
Me kake son cimma game da waka?
Gaskiya burikan da nake so na cimma a harkar waka suna da yawa amma alhamdullah na fara cimma wasu yanzu.
Ya ka dauki waka a wajenka?
Gaskiya ni na dauki waka sana’a ta.
Bayan sana’ar waka da kake, shin kana wata sana’ar ne?
Eh! ina da sana’ a bayan waka saboda ita waka lokaci ne da ita.
Taya kake iya hada aikin wakarka da kuma sana’ar da kake?
Ina yin kowacce, saboda kowacce na ware ma ta lokacinta.
Mene ne burinka na gaba game da waka?
Burina Allah ya kara daukaka ni a ko ina asan amo na.
Toh ya batun soyayya fa, ko akwai wadda ta taba kwanta maka a rai cikin masana’antar da har ta kai kun fara soyayya tare?
Gaskiya ban taba soyayya da wata a cikin masana’antar mu ba.
Idan wata ta ce tana sonka a cikin masana’antar shin za ka yarda ka aureta ko kuwa ba ka da ra’ayin hakan?
Eh! zan yarda in dai na yaba da kyawawan halayenta.
Yaushe za ka yi aure?
Eh! ina da burin yin aure nan kusa amma shi aure lokaci ne.
Wanne kira za ka yi ga masu kokarin shiga cikin masana’antar?
Kira na da masu kokarin shiga wannan harka su tabbatar sun shigo da amincewar iyayensu, sannan su shigo domin addininsu na Musulunci gudunmawa.
Wanne kira za ka yi ga sauran mawaka ‘yan uwanka?
Kirana ga sauran abokaina mawaka shi ne; mu dinga tsaftace harshenmu a cikin wakokinmu ban da batsa da zagi saboda ko bayan ka mutu idan an kunna wakarka a yi maka kyakkyawar addu’a.
Me za ka ce da ita kanta Jaridar Leadership Hausa?
Abin da zan cewa da wannan babban gidan Jarida na shi ne; Allah ya kara d a u k a k a shi, kuma dama ina jin dadin labaransu tun kafin na zo.