Connect with us

TATTAUNAWA

Dalilai Biyu Ne Ke Sa Malamai Tsoron Shiga Siyasa – Sheikh Khalil

Published

on

A tattaunawar da Editan LEADERSHIP A YAU LAHADI, NASIR S. GWANGWAZO, ya ke yi da fitaccen malamin addinin Islama kuma dan siyasa a jihar Kano, MALAM IBRAHIM KHALIL, duk mako, a wannan satin mun dora daga inda mu ka tsaya, inda malamin ya ke tsaka da bayani kan dalilan su ke hana malaman addini shiga siyasa a Najeriya. Ga yadda su ka dora:
To, kamar da ka bayar da misali da Farfesa Osinbajo cewa malamin addini ne, amma ba ka ganin kuma shi ya yi ilimin boko mai zurfi har ya kai matakin farfesa a fannin aikin lauya? Shin hakan bai bambanta sauran malaman addini da shi ba, domin su malamanmu na nan ba su yin ilimin boko, don haka ke ganin ba su cancanta ba?
Ah! Ka ga ka sake dauko daya ciwon. Koyaushe idan ka ji mutum ya na lakca zai ce ai babban abinda ya ke damun mu shi ne rashin ilimi. Da ka ce wane ilimin? Sai ya ce ilimin boko. Wato shi ilimin addini ba ilimi ba ne! Da me ilimin boko ya fi ilimin addini? Babu! Ko kusa da shi ma bai yi ba! Bai kai darajar ilimin addini ba! To, shi meye ilimin bokon? Ilimin boko ba shi da wata riga da ta fi ilimin addinin Musulunci kyau ko ta fi ta inganci ko ta fi ta komai. Ilimin boko ma gabadaya ai babu wani tsari na tarbiyya, kawai sai dai a karantar da kai tsari da ka’idoji da dokoki. Amma ba ta kai tarbiyya irin ta addini ba. Shi ya sa Obasanjo shi da kansa ya ce Najeriya ta na bukatar tarbiyyar addini, domin ya ce ‘spritual’. Don haka wannan ita ma wata farfaganda ce cewar ilimin karatun addini ba ilimi ba ne. Sai a ka mayar da shi ‘informal education’, ilimin boko shi ne ‘formal education’. Ka ga shi ma wata farfaganda ce, sannan shi Osinbajo farfesa ne na aikin lauya; a nan akwai lokacin da a ka rika cewa a fifita karatun kimiyya. Shi a ke kambamawa, don kawai a rushe wani tsari da a ke so a rushe, sai a ka ce a fifita ilimin kimiyya. To, ragowar ilimai kuma su lalace.
Duk a na yin haka ne don a kawar da wani abun. Sannan kuma da a ka ce a yi ta yin karatun bokon, shin shi karatun bokon da a ka ba shi daraja da muhimmanci har kowa shi ya ke so ya yi, me ya haifar na wani alheri ko cigaban da za a zo a na alfahari da shi? Wanda idan da ilimin addini ne ya sami goyon bayan, da ya haifar da abinda ba a tsammani. Mu abinda mu ke kira kullum shi ne a hada guda biyun, ilimn addini da ilimin boko. Amma raina ilimin addini a ce wanda ba shi da ilimin addini shi ne abin wofintarwa ba za a saurare shi ba, ba shi da hakki. To, yanzu China da Japan da Jamus da ragowar kasashe na duniya da fifita harshensu, sai ya zamana cewa su ba masu ilimi ba ne? Don haka farfaganda ce da niyyar mulkin mallaka, amma ta hikima. To, mutumin da bai san kansa ba, wannan mulkin mallakar ta ruwan sanyi sai ya cinye shi a yaki.

To, Malam duk da wadannan bayanai da ka yi, amma da yawa malaman addini ba su yarda su shiga siyasa tsundum. Shin kai me ya sa ka shiga kuma ba ka tsoron bayyana kanka a matsayin dan siyasa?
Saboda kishin kasata, Ina kishin al’ummata, Ina kishin addinina kuma Ina so na ga al’ummata ta na rayuwa irin rayuwar da Allah Ya halicci dan adam ya yi ta kuma na ga kasata ta na bayar da ma’anar da a ke nema a ko’ina a duniya. Su kuma ragowar malamai abinda ya sa ba sa son shiga siyasa abubuwa ne guda biyu. Da ganin cewa za a zagi mutum, za a ci mutuncinsu, za a yi mu su kage, za a yi mu su sharri, za a aibata su. Na biyu kuma shi ne cewar waccan farfaganda ta yi tasiri har ta kashe wa wasu malaman zuciyar da ko ka zo ka ce ma su yi, ba za su yi ba. Me ya sa a ka kashe mu su zuciya shi ne, abinda kawai a ka sa su a kai shi ne a kai su Makka su uyi ummara ko hajji, don su yi addu’a ko kuma a kira su domin su yi addu’a a wani gida ko su yi addu’a ga wani babban mutum.
Sai ya zamana cewa wannan hanya ce ta farfaganda ta a nukurkushe malamta ta tashi matsayinta na asali na jagoranci na shugabanci, domin shi malamin addini shi ne sama da kowa a duniya. To, sai a ka nukurkusa shi, don kada ya sake motsi kuma tauye martabar annabta ce, tauye martabar addini ne na Kirista ne ko na Musulunci, domin duk lokacin da a ka nukurkusa malami, to an nukurkushe addini da annabawa su ka zo da shi kuma an danne hakkin annabawa, an kuma danne hakkin da Ubangiji ya ke so ya fito ta hanya tsarkakakkiya.
To, wasu kuma za su ce da ma kai ka kan fita daban daga sauran malamai ko da a wajen fatawoyinka ne. Me za ka ce kan hakan?
A’a, ya danganta ga tsarin da mutum ya fahimta ko ya yarda da shi. Ni abinda na yarda da shi shi ne Ubangiji ya fada a Alkur’ani cewa Allah sauki ya ke nema gare ku, ba tsanani ba kuma Ubangiji ya ce ku zama masu saukakawa, Annabi ya ce ku zama masu saukakawa. Don haka saukin nan da Allah Ya gina dan adam a kansa, saukin nan da matsakaicin dan adam a kansa ya ke tafiya, sannan kuma da kokarin fahimtar meye Allah Ya ke nufi a addini da rayuwa, ban taba fita daga ka’idoji da manufofi na wannan ba. To, idan ya zamana kuma wani mutum ya sai wa kansa wata hanya, sai kuma a cewa ya za a yi. Misali, Abdullahi bin Umar a wani lokaci a na ganin fatawarsa ta na da tsauri, amma a fatawar Abdullahi bin Abbas a mafi yawan lokaci a na ganin ta na da sanyi da saukakawa har ma wasu su na ganin kamar saukin ma na son zuciya ne, amma sai an buga-an buga sai a ga cewa ashe ba na son zuciya ba ne. Wancan kuma tsaurin da ya ke yi, shi ma ba na son zuciya ba ne.
Wasu lokutan su malamai abinda su ke gani shi ne tsanantawa da takurawa shi ya ke sa wa mutane su bi Allah. Mu kuma mu na ganin a’a takurawa ba ta taba sawa an yi abu daidai ba, takurawa ba ta taba sa wa an bi Allah ba, takurawa ba ta taba sa mutum ya yi tunani mai kyau ba, takurawa ba ta taba sa mutum ya kai ga nasara ba. Idan da a ce takurawa ita ce ta fi kawo nasara, to da Allah da annabawansa sai su dora mutane a kan takurawa. Don haka abinda ya sa a ke ganin bambancin fahimta tsakanin wannan da wannan shi ne wane tsari mutum ya daukar wa kansa. Hanyar da kowa ya dauka, abinda a ke cewa ‘principle’, to kowa akwai wannan tsari da ya ke tafiya a kai ko wata manufa ko wata akida ko wata ka’ida, wacce ya tafi a kanta. To, kowa da yadda ya dauka. Kamar jam’iyyun siyasa na Amerika, ga Democratic ga Republican, kowacce da irin tsarin da ta ke tafiya a kai. Kusan jam’iyyun daya ne, amma akwai wani wuri da su ka sha bamban.
Kamar jam’iyyar da a ka yi na NRC da SDP kusan jam’iyyun daya ne, amma sai ka ji an ce ‘little to the right, little to the left’. Amma idan ka dube su kusan ma’anarsu daya ce. Kamar idan ka dauki PDP da APC dukkansu jam’iyyu ne na siyasa, amma za ka ga tsarin da su ke tafiya idan su ka samu gwamnati bambancin babu yawa. To, haka dan adam ya ke, koyaushe abubuwa su ke tafiya sai wannan ya ce wannan ya fiya zafi, wannan ya fiya sanyi. Ya danganta da me su ka fahimta, amma mu abinda mu ka yi imani da shi shi ne manufar da Allah Ya ke nufi da addininsa, manufar da Allah ya ke so dan adam ya rayu a kai da kuma abinda ya fi dacewa da talaka, domin talaka shi ne ma’auni. Komai idan ka na son ka gane kyansa da rashin kyansa samu mutumin da bai san komai ba, wanda ya ke ba a gina shi a nan ko can ba, ka tambaye shi. Ka tambayi mutumin kan titi, ka tambayi yaro, ka tambayi mutumin kauye. To, abinda za su fi fahimta su fi ganewa shi ne ya fi dacewa da rayuwa. Duk abinda ya shallake hankalin maras sani ko matsakaici a sani, to za ka ga ya haifar da wani abu wanda ba shi kenan ba.

Mu hadu a makon gobe in sha Allah, don jin cigaban wannan tattaunawar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: