Kungiyar masu kiwon kajin gidan gona ta kasa, reshen babban birnin tarayyar Abuja (PAN), ta yi kira ga Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya gaggauta kawo dauki, musamman wajen yawan samun hauhawar farashin abincin da ake ciyar da kajin gidan gona.
Kazalika, ta yi gargadin cewa, idan har ba a dauki matakin da ya kamata ba, ko shakka babu wannan fanni na kiwon kaji zai nakasu ta hanyar durkushewa baki-daya.
- Tsadar Magunguna Na Barazana Ga Rayukan Majinyata A Nijeriya
- Gwamatin Tarayya Ta Fito Da Tsarin Cin Gajiyar Ma’adanan da Ke Jihar Nasarawa
Sakataren kungiyar, Hakeem Musa ne ya yi wannan kira a babban birnin tarayya Abuja, inda ya nuna matukar damuwarsa a kan yadda ake ci gaba da fuskantar wannan hauhawar farashi na abincin kaji a daidai wannan lokaci.
Har ila yau, Musa ya yi nuni da cewa, ya kamata gwamnatin ta taikama musu a wannan sana’a tasu kiwon kaji na gidan gona, domin samun damar tsayuwa da kafafunsu.
Sakataren ya kuma buga misali da cewa, buhun abincin kajin mai dauyin kilo 25, a watan Nuwambar da ya gabata, an sayar da shi kan Naira 8,000, wanda daga baya kuma farashin budun ya karu zuwa Naira 9,100.
Ya ci gaba da cewa, a makon farko na watan Disambar da ya gabata, farashin budun ya karu zuwa Naira 9,350 daga bisani kuma a makon farko farashin ya kai Naira 9,550, wanda kuma a mako na uku farashin ya karu zuwa Naira 10,950.
Hakeem ya kara da cewa, babu wanda ke da masaniyar lokacin da wannan farashi na abincin kaji zai daina yin tashin gwaron zabi.
Sai dai, sakataren ya bayyana fatan cewa, Gwamnatin Tinubu za ta mayar da hankali wajen bunkasa wannan fanni da kuma samar musu da tallafi .
A cewar tasa, mun fi bukatar a samar mana da tallafin kudi, domin ci gaba da tafiyar da wannan sana’a tamu.
Sannan kuma ya danganta wannan karanci na kaji a kan matsalar hauhawar farashin abincin kajin, musamman masara da waken suya, wadanda ake amfani da su wajen hadawa tare da sarrafa abincin kajin.
A karshe, Sakataren ya bayyana cewa, hauhawar farashin abincin kajin, na matukar haifar wa masu wannan sana’a nakasu, wanda hakan ne ke jawo wa wasunsu suke dakatar da yin sana’ar baki-daya.