A watan Fabrairu na wannan shekarar, fusatattun matasa suka mamaye titunan garin Minna babban birnin Jihar Neja da wasu kuma matasan a Kano da suka gudanar da zanga-zanga a kan abin da suka kira tsadar rayuwa a kasar nan.Irin wannan zanga-zangar ta kuma barke a Jihar Ondo da wasu sassan kudu masu yammacin kasar nan.
Kungiyoyin addini sun lura da cewa rayuwa ga talaka a Nijeriya tana kara tsauwwala musamman abin da ya shafi farashin kayan abinci da kudin sufuri da kuma sauran al’amurran yau da kullum duk suna neman su gagari yawancin ‘yan Nijeriya.
- Za A Bude Shafin Karbar Bashin Dalibai A Ranar 24 Ga Mayu
- Sin: Karbuwar Hajojin Sin Masu Nasaba Da Sabbin Makamashi Ba Shi Da Nasaba Da Samar Da Tallafi
Kungiyar Kiristoci ta kasa CAN ta bayyana cewa, al’amarin yana kara ta’azarra ne sakamakon matsalar tsaro da ake fama da ita wanda kuma shi ya haifar da kashe-kashe da kuma garkuwa da mutane don mena kudin fansa.
Idan za a iya tunawa, wannan jaridar ta ruwaito cewa, mai alfarma Sultan na Sakkwato, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar lll wanda kuma shi ne shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ya bukaci gwamnatocin tarayya da na jihohi su gaggauta kawo dauki domin magance matsalar tsadar rayuwa wadda ita ce ta tunzura al’umma yin zanga-zanga a wasu sassan Nijeriya.
Kasar nan tana fuskantar matsanancin tattalin arziki da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin Nijeriya, al’umma na fama da talauci da tashin hankali a kowane lungu da sako na kasa.
A yayin da wannan gwamnatin ke neman cika shekara daya da dare wa kan karagar mulki,mun lura cewa,babu wani abin da ya canja a cikin wannan shekarar sai da karin talauci da yunwa a tsakanin ‘yan Nijeriya.
Shugaban kasa Tinubu ya janye tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayu 2024 yayin da aka tanstar da shi a matsayin shugaban kasa daga nan farashin man fetur ya yi tashi da ninkin baninkin 300 hakan kuma shi ya haifar da hauhawar farashin kayan abinci da sauran kayan amfani na yau da kullum.
Karuwar farashin man fetur da aka samu ta haifar da tsadar kayayyakin aiki ga kamfanoni da kuma kudin zirga-zirga haka kuma ya kai ga dora wadannan kudaden a kan talakawa masu amfani da kayan da kamfanonin ke sarrafawa.
Karuwar yanwa ta kuma haifar da tashin hankali a tsakanin matasa, har an fara samun fusasasstun matasa da suke tare hanya suna wasoson kayan abinci, dukkan wadannan kuma sakamakon tsare-tsare ne na Shugaban Kasa Bola Tinubu, musamman tsarinsa na karya darajar naira.
Sakamakon wadannan manufofin ne na tsare-tsaren tattalin arzikin Shugaba Tinubu ya haifar da matsanancin wahalar rayuwa ga al’ummar Nijeriya gaba daya.
Farashin kayan masarufi sun yi tashin gwauron zabo, kayan abinci kamar shinkafa,wake, masara tumatur da sauransu sun tashi da kashi 25.34 zuwa 40.01 a kididdigar da aka yi a watan Maris na shekarar 2024.
Ana cikin wannan matsin ne na tattalin arzikin sai kuma ga shi gwamnati ta kara kudin wutar lantarki da kashi 603 inda ya zama naira 225 a kan kilowat daya.
Duk da wannan karin ba wai ana samun wutan lantarkin yadda ya kamata ba ne,hakan kuma ya kai durkushewar kananan masana’antu da dama.
Babu ko kokwanto, mastalar tattalin arzikin da ake fama da ita a halin yanzu, tsanannin talauci da tsadar farashin abinci suna yin barazana ga rayuwar talakan Nijeriya.
Tsadar rayuwa na ci gaba da takura ‘yan Nijeriya,musamman matasa wadanda ke hankoron barin kasar domin samun ingantaccen rayuwa a kasashen waje.
A wani binciike da wata kungiya mai zaman kanta mai suna NOIPolls ta gudanar a watan Agusta na 2024 ta gano cewa kashi 63 na ‘yan Nijeriya a fadin kasar nan a shirye suke su yi kaura zuwa kasashen waje in sun samu damar yin haka.
Binciken ya kuma gano cewa matasa masu shekaru tsakanin 18 zuwa 35 sune a kan gaba wajen neman hanyar yin kaura zuwa kasashen waje.
Binciken ya kuma gano cewa, kashi 60 na masu neman fita kasashen waje suna yi ne domin samun ingantacciyar rayuwa a kasashen waje.
Amma kashi 3 na masu hankoron fita sun bayyana matsalar tsaro a matsayin dalilin su na neman fita kasashen waje.
A halin yanzu yunwa da matsalar tsaro na ci gaba da wahalar da ‘yan Nijeriya sai kuma ga hauhawar farashi ya kara kunno kai,tabbas al’umma na cikin wahala a Nijeriya.
Duk bangaren da ka duba a Nijeriya zaka lura da yadda garkuwa da mutane, ta’addanci, harkokin ‘yan bindiga suke aukuwa a kullum garin Allah ya waye.
Ci gaba da tabarbarewar darajar naira da kuma yadda gwamnati ta kasa shawo kan lamarin ya kara jefa ‘yan Nijeriya cikin halin ni ‘yasu.
Yayin da lamarin yake kara ta’azzara,dole gwamnati ta gaggauta daukar matakan ta yin maganin matsalar tattalin arzikin da ake fuskanta da kuma matsalar tsaro a sassan Nijeriya wadanda sune suka haifar da tsadar rayuwa ga talakawa.