Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, gwamnatinsa za ta narkar da dala biliyan 1.96 wajen gudanar da aikin jirgin kasa a tsakanin Kano zuwa Maradi ne domin bunkasa ayyukan tattalin arziki da inganta zirga-zigan matafiya musamman ma wajen saukaka zirga-zirgan kayayyakin noma da sauran ma’adanai wanda kamfanoni suke bukata domin su sarrafa su. Buhari ya bayyana hakan ne a wajen taron bayar da ba’asi a kan aikin jirgin kasan tsakanin Kano zuwa Maradi wanda ya gudana a garin Katsina a ranar Talata.
A cewar shugaban kasan, idan aka samu nasarar kammala aikin, zai saukaka gudanar da zirga-zirgan kayayyaki a cikin gida Nijeriya zuwa kasar Jamhuriyar Nijar ta hanyar jiragen kasa, wannan aiki zai yi matukar kawo wa Nijeriya da kasar Nijar makudan kudaden shiga a kasuwancin harkokin sufuri na cikin gida na waje. Ya kara da cewa, titin jirgin ya hade jihohi masu yawa tare da wasu yawankuna tun daga Kano da Kazaure da Daura da Kastina da Jibiya da kuma Maradi da ke Jamhuriyar Nijar, wanda mutane miliyan 800 za su amfana da wannan aiki.
Tun da farko a wajen taron, gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya yaba wa shugaban kasa wajen gudanar da wannan gagarumin aikin titin jirgi wanda ya hada kasa da kasa, domin saukaka hanyoyin gudanar da harkokin sufuri a tsakanin kasashe guda biyu wato Nijeriya da kuma Jamhuriyar Nijar. Masari ya bayyana cewa, titin jirgi da ke tsakanin Ibadan zuwa Kano wanda aka kammala da kuma wanda yah ade Kano da Maradi a Jamhuriyar Nijar wanda ake yi a yanzu za su taimaka wajen rarraba kayayyaki a cikin kasar nan. Haka kuma, ya yaba wa ma’aikatar sufuri da kamfanin Mota – Engil wanda suka tabbatar da sa’ida tare da bayar da tabbatar da ganin an kammala aikin a kafin shekarar 2023.
A nasa jawabin, ministan sufuri, Rt. Hon. Chibuike Amaechi ya bayyana cewa, titin jirgin kasa da ke tsakanin Kano da Maradi, waanda tashar ta hade garuruwa kamar haka Kano da Kastina da Kazaure da Daura da Jibiya da kuma Duste. Ya tabbatar da cewa, aikin zai kammala ne a shekarar 2023, wanda zai dunga jigilar fasinjoji guda 9,300 a duk kullum tare da kayayyaki mai nauyin tan 3,000 tun daga Kano zuwa Maradi. Amaechi kara da cewa, wannan aiki na titun jirgin kasa tsakanin Kano zuwa Maradi an fara gudanar da shi ne tun a shekarar 2012 aka samu takardar shaidai aiki, amma an fara gudanar da asalin aikin ne a shekarar 2015. Ya ce, wannan gagarumin aiki ne da gwamnati ta barko wanda zai yi matukar farfado da tattalin arziki. Ya ci gaba da cewa, ana bukatar irin wannan aikin tun da tsawan lokaci a Nijeriya.