Jam’iyyar NNPP ta bayyana dalilan da suka sa dan takararta na shugaban kasa, Rabiu Kwankwaso, bai taya zababben shugaban kasa, Bola Tinubu murna ba.
NNPP ta ce Kwankwaso bai taya Tinubu murna ba saboda zaben shugaban kasa bai taka rawar da ta dace ba.
- Zaben Shugaban Kasa: Tinubu Ya Bukaci Kotu Ta Ba Shi Damar Duba Kayayyakin Zabe
- APC Ta Dauko Manyan Lauyoyin 12 Da Za Su Kare Nasarar Da Tinubu Ya Samu A Zabe
Wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na NNPP, Agbo Major, ya fitar, ta ce rahotannin da ke yawo cewa Kwankwaso ya taya Tinubu murna ne na hasashe na masu adawa da dimokuradiyya, ma’aikatan siyasa da ’yan jarida.
Major ya ce jam’iyyar ta ki amincewa da sakamakon zaben ne saboda bai dace da buri ‘yan Nijeriya da suka fito domin kada kuri’a ba.
A cewar Major: “Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, bai taya dan takarar jam’iyyar WPC, Bola Tinubu murnar lashe zaben shugaban kasa da aka yi mai cike da kura-kurai, rigima da takaddama.
“NNPP ta ki amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga Fabrairu, 2023, saboda gazawar INEC wajen gudanar da sahihin zabe.
Ya kara da cewa: “Ba zato ba tsammani Kwankwaso zai yi gaggawar taya Asiwaju Tinubu murna kan wa’adinsa da ake ta tantama wanda sauran ‘yan takarar su ma suka yi ikirarin cewa sun yi nasara kuma sun garzaya kotu domin neman hakkinsu.