Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce bai halarci taron Kungiyar Lauyoyin Nijeriya da ta gayyace shi ba, sakamakon wasu muhimman ayyuka da suka sha gabansa.
Wannan na dauke ne cikin wata wasika da ya aike wa kungiyar lauyoyin ta NBA, wacce kakakinsa Abdulmumin Jibril kofa, ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso, ya bai wa kungiyar hakuri bisa rashin samun damar halartar taron nata.
- Wayar Salula Ta Haddasa Gobara A Gidan Mai A Legas
- “Ɗaukar Abdulkarim Daura Matsayin Mataimakin Gwamna Zai Kawo Wa APC Nasara A Katsina”
“Ina so na bayyana cewa na samu wasikar gayyatarku, mai dauke da maudi’in da ya gabata, ina kuma so na sanar da ku cewa ban samu damar halartar wannan taro mai muhimmanci ba, saboda wasu muhimman abubuwa da ke gabana da suka shafi kasa,” in ji Kwankwaso.
A cikin wasikar, Kwankwaso ya ce, abokin takararsa Bishop Isaac Idahosa ya fita kasar waje, “amma da na turo shi don ya wakilce ni.”
A ranar Litinin ne NBA ta bude babban taronta na kasa a karo na 62 a Jihar Legas.
Taron ya samu halartar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi da kuma mataimakin dan takararar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, Kashim Shettima.
Shi ma dan takarar jam’iyya mai mulki ta APC, Bola Ahmed Tinubu, bai samu halatar taron ba, amma ya tura abokin takararsa Kashim Shettima don ya wakilce shi.
Ire-iren wadannan taruka kan gayyaci ‘yan takarar mukamin shugaban kasa don su bayyana wa jama’a manufofinsu kan yadda za su tunkari matsalolin kasa.
Rashin zuwan na Kwankwaso ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta, inda kowa ke tofa albarkacin bakinsa.