Babu ko shakka daukacin masu bukatu na musamman da su ke karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna, Allah ya tallafa ma su da Dan Isan Zazzau, Alhaji Umar Shehu Idris da ya tashi tsaye dare da rana, domin share ma su hawaye day a shafi matsalolin da su ke fuskanta.
Shugabar kungiyar guragu na karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna, Malama Rukayya Aliyu ta bayyana kalaman da su ka gabata a lokacin da suka kammala taron kungiyarsu a Zariya.
Malama Rukayya Aliyu ta cigaba da cewar, wannan bawan Allah Dan Isan Zazzau, musamman ya shaida wa kungiyar masu bukatu na musamman a lokacin da su ka ziyarce a ofishinsa da ke fadar Zazzau a karshen makon da ya gabata.
Ta cigaba da cewar, tun daga lokacin da Dan Isan Zazzau ya yunkura ya fara tallafa wa ma su bukatu na musamman a masarautar Zazzau, ba karamar hukumar Zariya kawai ba, ma su bukatu na msun fara samun mafita a matsaloli da dama da su ke matukar addabar su, da su ka hada da cigaba da ilimi da kuma sana’o’in dogaro da kai da masu bukatu na musamman ke son yi, amma, tsadar rayuwar da a ke ciki a yau, ta sa dole sun saw a sarautar Allah ido.
Malama Rukayya Aliyu ya kara da cewar, babu ko shakka, a yanzu, masu bukatu na musamman sun sami natsuwa tun daga lokacin da Dan Isan Zazzau Alhaji Umar Shehu Idris ya fara tallafa wa ‘ya’yan kungiyar da su ke sassa daban daban na masarautar Zazzau.
A dai zantawar ta wakilinmu, Malama Rukayya ta kuma yi amfani da damar da ta samuu, inda ta yi kira ga sauran al’umma da su yi koyi da Dan Isan Zazzau na tallafa wa ma su bukatu na musamman kamar yadda Dan Isan Zazzau, Alhaji Umar Shehu Idris ke yi.
A cewarta , babu ko shakka, babu wani dan siyasa da ke tallafa wa kungiyar ma su bukatu na musamman a karamar hukumar Zariya, musamman in duba yadda ‘ya’yan sun bayar da gudunmuwar a lokutan zabubbukan da su ka gabata, tun daga shekara ta 1999 zuwa shekara ta 2019.
Da kuma Malama Rukayya Aliyu ta koma ga mambobin kungiyarsu, wato ma su bukatu na musamman, sai ta jawo hankalinsu na wajibi ne das u rika amfani da duk wani tallafi da suka samu, wajen ci gaba da karatu ko kuma ci gaba da sana’o’in dogaro da kai, da za su katange su daga yin barace – barace da gwamnatoci ke niyyar hana wa, bayan babu wasu wasu tsare-tsaren da gwamnatocin suka yi, in ma an yi, a cewar ta, za ka cimma tsare-tsaren a takarda kawai aka yi su, wajen aiwatarwa, a wannan mataki ake samun matsala ko kuma matsaloli.