Wani dan jarida mai jin harsuna biyu, Alhassan Bala, ya karkiro da wata manhajar binciko gaskiya da sahihancin lamura da ya yi wa suna da ‘Alkalanci’ (The Arbiter).
Manhajar wacce ta maida hankali wajen gano gaskiya da hakikanin ikirarorin lafiya, harkokin siyasa da wasu bangarori daban-daban dukka a cikin harshen Hausa.
- Xi Ya Amsa Wasikar Wakilan Daliban Da Suka Halarci Gasar Kere-Keren Kimiyya Ta Kasa Da Kasa Ta Kasar Sin
- Ɗaliban Kwalejin Kimiyya Ta Jega Sun Yi Zanga-Zanga Har Da Ƙone-Ƙone
Babban manufar samar da manhajar shi ne, domin a taimaka wajen kare mutane daga fadawa tarkon ‘yan damfara da masu yada karya a tsakanin jama’a.
Karin tagomashi kan wannan manhajar shi ne, za ta taimaka kuma wajen gano gaskiya ko sahihancin hotuna da bidiyoyi domin wayar da kan masu karatu da harshen Hausa a kasar Nijeriya, Kamaru, Ghana domin cire kokwonto ko shakku kan hotuna ko bidiyo na karya ko na gaskiya.
Wannan lamarin ya zo a kan gaba kuma zai taimaka matuka gaya musamman yadda a irin wannan lokacin wasu mutane suka dukufa na amfani da ‘photoshop’ da kirkirarriyar basirar (AI) wajen hada hotuna da bidiyo na bogi domin shagaltar da hankulan jama’a ko neman kudin daga wajensu.
“Mun nazarci duniyar fasahar zamani, kuma mun gano yadda masu amfani da kafafen fasahar zamani da harshen Hausa ke amfani wajen shagaltar da hankula da yada karerayi a tsakanin masu jin harshen Hausa.
“Sannan ana yawan samun ikirarin yawan rashin lafiya na karya da kuma jama’a su na yarda da hakan.
“Don haka ya zama abu mai muhimmanci a garemu da mu samar da manhajar da za ta jagoranci wayar da kan masu jin harshen Hausa,” kamar yadda Bala ya shaida ta cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi.
Dan jarida ya ci gaba da cewa, “Manhajar ‘Alkalanci’ za mu dukufa wajen ilmantar da mutane kan yadda za su kare kansu daga fadawa tarkon ‘yan damfara da masu yaudara ko masu yada bayanan karya ko shaci fadi, hotuna da bidiyo.”
Alhassan Bala, wanda ya shafe shekaru masu yawa yana aikin jarida a kafafen yada labarai daban-daban, yanzu haka yana aikin jarida ne a gidan rediyon Muryar Amurka na sashin Hausa da na Ingilishi.