Dan majalisar dokokin Jihar Kano, Labaran Madari, daga mazabar Warawa a jam’iyyar APC, ya dauki malaman wucin gadi 105 domin bunkasa ilimi a mazabarsa.
Mista Madari ya gabatar da wasikar daukar aikin ga sabbin malaman da aka dauka a ranar Laraba a Warawa.
- Ranar Malamai Ta Duniya: Yadda Yajin Aikin ASUU Ya Yi Wa Ilimi Katutu A Wuya
- Zargin Badakalar Kudade: Kotu Ta Wanke Magu
Ya ce an yi hakan ne domin a kara yawan malamai da kuma rage rashin aikin yi a tsakanin al’umma.
Dan majalisar wanda kuma shi ne shugaban masu rinjaye ya yabawa gwamna Abdullahi Ganduje bisa bullo da tsarin ilimin kyauta kuma dole a jihar.
Mista Madari ya kara da cewa, akwai bukatar a gaggauta ba da gudummawar kasonsa don samun nasarar manufofin.
Dan majalisar ya bayyana cewa yana cikin tawagar da suka yi nasarar bullo da shirin bayar da ilimi kyauta kuma tilas ga yara da Ganduje ya yi.
Mista Madari, ya ce ya gina azuzuwa 35 da bandaki 11 a makarantun Firamare da Sakandare da Islamiyya.
Shugaban masu rinjayen, ya kara da cewa ya samar da kayan koyo da koyarwa, da kuma kammala ga makarantar sakandaren ‘yan mata, da ke Warawa da dai sauransu.
“Ina so in tabbatar muku da kudirina na kare muradunku ga majalisar don samar da ribar dimokuradiyya,” in ji shi.
Mista Madari, ya ce za a rika biyan malaman alawus-alawus duk wata kuma za a bi diddigin yadda gwamnatin jihar za ta karbe su a matsayin malamai na dindindin da kuma karbar fansho.
Kwamishinan Ilimi, Ya’u Yan’shana, wanda ya bayyana shirin a matsayin wanda ya dace, ya yabawa dan majalisar bisa wannan karimcin da ya yi.
Kwamishinan ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na samar da ilimi kyauta.
Ya kuma bukaci masu hannu da shuni da su bayar da tasu gudunmawarsu ta hanyar daukar malamai aiki ga al’ummarsu.
Shugaban hukumar kula da ilimin bai daya na Jihar Kano (SUBEB), Danlami Hayyo, ya jaddada kudirin hukumar na horar da sabbin malaman domin cimma burin da ake so.
Mista Hayyo ya ce shiga tsakani zai taimaka matuka wajen habaka ilimi a matakin farko, inda ya ce bangaren ilimi na bukatar karin irin wannan kokari.
Sakataren ilimi na karamar hukumar Warawa, Ibrahim Idris ya ce an yi amfani da samfuri wajen zabar kwararrun masu matakin ilimi na NCE, a unguwanni 15 na karamar hukumar.