Dan Nijeriya Ya Sayi Motar Gwamnan Amurka

Wani dan Nijeriya, ya sayi motar shahararen jarumin fina finan Hollywood din nan, Arnold Schwarzenegger.

Obi Okeke, da aka fi sani da Dakta Bugatti, ya sayi motar Mista Schwarzenegger kirar Bugatti beyron a kan kudi dala miliyan biyu da dubu dari biyar.

A cewar jaridar, Mista Okeke, wanda dillalin motocin Bugatti ne, ya ce yana da aniyar sayar da motar.

Mista Okeke dai, na da kwastomomi sosai masu hannu da shuni , ciki har da dan wasan dambe Floyd Mayweather.

Wata jaridar wasanni ta kasar Spaniya da ake kira Top Gear, ta wallafa labarin Mista Okeke, inda ta yi masa lakabi da mutumin da ke iya sayar da motocci 93 a lokaci guda.

An Sami Giwar Ruwan Da Ta Fara Magana A Duniya

An samu wata muguwar giwar ruwa da ke iya kwaikwayon maganar mutane har ta fadi kalmomi kamar ”halo” da ”bai-bai” wadda ake ganin irinta ce ta farko da ke iya haka.

Giwar ruwan ta koyi fadar wasu kalmomi na maganar mutane ta hanyar kwaikwayon mai horad da ita a wani kebabben tafkin halittun ruwa a Faransa.

Kalmomin da wannan katuwar dabbar ruwa ke iya fade sun hada da sunan “Amy” da kirgen Ingilishi “one, two, three”.

Giwar ruwa da kifi nau’in ”dolphins” na daga ‘yan kalilan din dabbobi ko halittu bayan mutane da suke iya fadar wata kalma sabuwa daga jin an fade ta.

“Wannan abu ne da ba a saba gani ba a tsakanin dabbobi masu shayar da nono,” in ji Dakta Josep Call na Jami’ar St Andrews, daya daga cikin wadanda suka gudanar da binciken.

Ya ce: “Ba shakka mutane sun kware da yin haka, (wato maimaita kalma da zarar sun ji ta a karon farko), kuma abin ban sha’awa dabbobi ko halittun ruwa masu shayar da nono su ne suka fi iya haka a tsakanin dabbobi masu shayarwar.”

Daga nan ne sai masu binciken suka dukufa wajen gano ko irin giwar ruwan nan mai hadarin gaske za ta iya koyar fadar kalmomi idan aka furta mata ta hanyar kwaikwayon wanda ya fada.

Masanan sun yi gwaji da wata giwar ruwa mai suna Wikie a tafkin Marineland Akuarium a Antibes da ke Faransa.

An koya mata yadda za ta furta wasu kalmomi na mutane da hancinta wadanda aka saurari yadda ta maimaita su ta hanyar nadar sautin da ta futar bayan an furta mata su, kalmomin sun hada da ”hello” da ”Amy” da kirgen ”one, two, three”.

An san wannan dabba, muguwar giwar ruwa da rayuwa a cikin halittun ruwa da ke da baiwar furta kalmomi na musamman. Dabbar tana iya kwaikwayon sautin da wasu dabbobin irinta suke furtawa, ko da yake akwai bukatar a tantance hakan.

“Wannan giwar ruwan da aka gudanar da binciken a kanta tana iya koyon wasu kalmomi ko sautin da ‘yan uwanta suke yi da kuma sautin da mutane ke furtawa ta hanyar kwaikwayo,” in ji Dakta Call.

“Wannan sakamakon ya nuna yadda wannan nau’in giwar ruwa a teku take iya koyon sauti ko furucin da sauran ire-irenta suke yi, da kuma yadda daga nan za ta samar da irin nata karin sautin.”

Kwaikwayon magana wata baiwa ce da ‘yan adam ke da ita, amma a kan samu hakan a tsakanin wasu dabbobin jefi-jefi.

Wani nau’in kifin dolphin da kuma giwar ruwa suna daga cikin dabbobi masu shayarwa da ke iya kwaikwayon sautin wasu dabbobin daban,

Tsuntsaye ma suna kwaikwayon maganar dan adam musamman aku da wasu dangogin hankaki.

Dakta Jose Abramson, na jami’ar Complutense Unibersity da ke Madrid a Sipaniya, wanda na daga cikin wadanda suka gudanar da binciken, ya ce, akwai yiwuwar wata rana a iya tattaunawa mara wahala da giwar ruwa.

Giwar ruwa na daga cikin dabbobi mafiya karfin farauta a duniya.

Su na cinye dabbobin ruwa daban-daban ciki har da manya-manyan masu hadarin gaske.

Exit mobile version