Wani dan sanda a Jihar Kebbi ya daba wa abokin aikinsa almakashi har lahira sakamakon mugun musu.
ASP Shu’aibu Sani-Malunfashi, an ce mataimakin Sufetan ‘yansanda (ASP), Abdullahi Garba, abokin aikinsa ne ya daba masa wuka a hakarkarinsa na hagu da almakashi.
DSP Nafi’u Abubakar, kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Kebbi, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa jami’an biyu sun samu sabani da ya rikide zuwa fada a gaban shagon Garba.
A cewar kakakin, an fara gudanar da bincike kan lamarin kamar yadda Ahmed Magaji-Kontagora, kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kebbi ya bayar da umarni.
Sanarwar ta bayyana cewa, CP ya yi Allah-wadai da wannan mummunan lamari, inda ta bayyana shi a matsayin wanda ya saba wa horon aikin ‘yansanda, ayyuka da ka’idojin rundunar ‘yansanda, da kuma sauran dokokin da suka shafi Tarayyar Nijeriya.
Sanarwar ta kara da cewa, “Lamarin ya faru ne a ranar 1 ga watan Oktoba, 2022. A yayin da ake tsaka da abun, ASP Abdullahi Garba ya caka wa ASP Shu’aibu Sani-Malunfashi almakashi a hakarkarinsa na hagu.”
Bayan samun rahoton, sanarwar ta bayyana cewa DPO Argungu, ya garzaya wurin da lamarin ya faru, inda ya damke jami’in da ya aikata laifin, sannan ya kwace makamin.
Ya kara da cewa shi (DPO) ya garzaya da Sani-Malunfashi zuwa asibitin Sir Yahaya da ke Birnin Kebbi, inda wani likita ya tabbatar da rasuwarsa.
Sanarwar ta bayyana cewa, nan take aka kama Garba tare da tsare shi a sashen binciken manyan laifuka na jihar (CID), Birnin Kebbi, inda ta ce an kuma mika karar zuwa sashen kisan kai domin gudanar da bincike mai zurfi domin gano mumunan lamarin.