Al’ummar Igbogene da ke karamar hukumar Yenagoa a Jihar Bayelsa sun shiga makoki a yammacin ranar Litinin yayin da wani matashi dan shekara 16 mai suna Temedi Agbede Yerimene ya nutse a ruwa.
An ce Yerimene ya tafi ninkaya ne a kofar shiga cibiyar kula da lafiya ta jihar a lokacin da ruwan ya tafi da shi.
- ‘Yan Bindiga Sun Kone Hedikwatar Karamar Hukuma A Ebonyi
- Sojoji Sun Damke Fakitin Tabar Wiwi 98 A Yobe
Wani ganau ya shaida wa Daily Trust cewa an jawo gawar yaron ne a cikin magudanar ruwa da ke kusa da titin Bayelsa Gateway, da ke kan titin Gabas zuwa Yamma.
Ya ce kokarin da jami’an ‘yansandan suka yi na gano gawarsa ya ci tura yayin da jama’a ke fafutukar tserewa daga yqnkin saboda yadda ruwan ke kara ballewa.
Mahaifiyar matashin wadda ta bayyana kanta a matsayin Mama Carol ta tabbatar da faruwar lamarin.
Ta ce: “Na je kasuwa ne don in samo kayan abincin rana. Da na dawo daga kasuwa, sai aka ce min ya tafi iyo tare da abokansa.
“Amma na yi tsammanin babu wani abu da zai faru. Har sai da wani abokinsa ya sanar da ni cewa ruwa ya yi awon gaba da shi.”
Tuni dai gwamnatin jihar a makon da ya gabata ta rufe makarantu a jihar domin tseretar da dalibai daga mamakom ambaliyar ruwa da jihar ke fama da shi.
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya ce har yanzu ba a kai rahoton lamarin ga ‘yansanda ba har zuwa safiyar ranar Talata, amma ya yi alkawarin gano bakin zaren ta bakin jami’in ‘yansanda da ke kula da yankin.