Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya ce abotar dake tsakanin Sin da Afrika ta kara karfi yayin da aka fuskanci kalubalen COVID-19 a shekarar 2020.
Wang Yi ya bayyana haka ne yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua da kuma babban gidan rediyo da talabijin na kasar (CMG).
Ya ce a matsayinsu na kasashe masu tasowa, Sin da Afrika na da hakkin ingiza muradun kasashe masu tasowa.
Ya kara da cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugabannin Afrika, sun yi nasarar gudanar da taron koli kan karfafa goyon bayan juna wajen yaki da COVID-19, kana an karfafa al’adar taimakekeniya dake tsakaninsu.
Har ila yau, ya ce kasar Sin ta tura tawagar jami’an lafiya zuwa nahiyar Afrika, an kuma yi hadin gwiwa tsakanin asibitocin bangarorin biyu, baya ga samar da kayayyakin lafiya da ake matukar bukata da kuma hada hannu da nahiyar wajen samar da riga kafi. Bugu da kari, Ya ce a baya-bayan nan aka aza harsashin tubalin ginin hedkwatar cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Afrika CDC karkashin tallafin kasar Sin, yana mai cewa, aikin zai kasance babbar alama ta hadin gwiwar bangarorin biyu wajen yaki da annobar COVID-19.
Wang Yi ya kuma bayyana cewa, Sin da Afrika suna kara aiwatar da abubuwan da aka cimma yayin taron tattauna hadin gwiwar bangarorin biyu wato FOCAC, inda aka fi bada muhimmanci ga shirin kiwon lafiya.
Ban da wannan, ya ce Sin ta rattaba hannu kan yarjejeniyar jinkirta lokacin biyan bashi ga wasu kasashen nahiyar 12, kana ta yafe wasu basussuka marasa kudin ruwa ga kasashe 15, inda ya ce Sin ce ta fi bada rangwamen biyan bashi fiye da dukkan mambobin kungiyar G20.
Ya ce yayin taron FOCAC da za a gudanar bana a kasar Senegal, Sin da Afrika za su mayar da hankali kan wasu bangarori 3 da suka hada da hadin gwiwa wajen samar da riga kafin COVID-19 da farfadowar tattalin arziki da samar da ci gaba, domin cimma sabuwar matsayar goyon bayan juna da bude sabon babin hadin gwiwa da samar da karin moriya ga jama’a. (Fa’iza Mustapha)