ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, November 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dannau Ba Matsalar Aljanu Ba Ce, Aikin Kwakwalwa Ne -Dakta Maryam (Adon Gari)

by Najib Sani
3 years ago
maryam

Wata masaniyar aikin likitanci ‘yar asalin Jihar Bauchi da ke zaune a Birnin Tarayya Abuja, Dakta Maryam Almustapha ta warware tunanin da jama’a da dama ke yi na cewa matsalar Dannau a lokacin tashi daga bacci aljanu ne ke haifar da shi, wanda ake ganin kamar aljanu ne ke danne mutum, tana mai nuni da cewa matsala ce da kwakwalwa ke haddasawa.

A hirar da ta yi da jaridar LEADERSHIP, Dakta Maryam ta bayyana cewa matsalar Dannau tana sanya mutum ya kasa motsi a lokacin da ya farka daga bacci, wanda hakan kai tsaye aikin kwakwalwa ne da tsokokin jiki (Muscles).

  • A Nijeriya Idan Ka Ce Za Ka Rike Aikin Gwamnati Shi Kadai Akwai Kalubale – Fatima (Adon Gari)

Ta ce matsalar wacce take iya firgita wanda ya samu kansa a ciki, ta kan saka mutum ba kawai ya kasa motsi ba, har ma ya gagara numfashi duk da cewa yana farke a gadonsa kuma yana cikin hankalinsa.

ADVERTISEMENT

“Matsala ce da ta kan auku ga mutane da yawa wacce kan sa mutum ya kasa motsi, yin numfashi da kuma gane-gane da jiye-jiye”, in ji ta.

Ta ce matsalar za ta iya faruwa ga mutum kafin ya yi bacci ko bayan ya farka kuma za ta iya daukar dakikoki ko wasu mintuna kafin ya saki mutum, tana mai karawa da cewa Dannau ya zamo ruwan dare cikin al’umma yadda in ka samu mutum 100, akalla mutum hudu su kan fuskanci matsalar daga lokaci zuwa lokaci.

LABARAI MASU NASABA

Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba

Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna

Dadin dadawa, Dakta Maryam ta ce bacci ya kasu kashi biyu; da bacci mai nauyi da ake kira da ‘REM sleep’ da mara nauyi wanda ake kira da ‘non REM sleep’ a turance.

maryam
Dakta Maryam

Masaniyar aikin likitancin ta cigaba da cewa a lokacin bacci mai nauyi ne mutane suke mafarki wanda yake sanya kwakwalwa ta kashe tsokokin jiki don hana mutum ya buga jikinsa ko kuma ya fado kasa daga gado sakamakon motsawar jikinsa lokacin da yake mafarki.

Maryam ta ce matsalar Dannau ta kan faru ne idan kwakwalwa ta ki kunna tsokokin jiki don su cigaba da motsi bayan mutum ya farka daga bacci, sannan kuma ba a gano hakikanin abin da yake janyo matsalar Dannau ba lokacin farkawa daga bacci.

Sai dai ta ce wasu daga cikin abubuwan da suke janyo matsalar sun hada da mutum ya yi bacci a kan bayansa, rashin yin bacci akai-akai, shan giya da sauran kayan da suke sa maye, yin gadon matsalar daga dangi, gajiya, damuwa, da tsoro za su iya haddasa ta.

Da take bayyana cewa Dannau baya da magani, akwai abubuwan da in mutum ya kiyaye zai guje wa fuskantar matsalar.

Abubuwan sun hada da daina kwanciya ta baya, kauracewa wa shan giya, yin bacci akai-akai, yin bacci lokacin da ka saba yi, samun isasshen bacci kamar awa shida zuwa takwas ko wace rana, kashe wuta da rage sauti mai hana bacci lokacin da mutum zai kwanta.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba
Manyan Labarai

Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba

November 12, 2025
Majalisa Na Binciken Kwangilar Titin Naira Biliyan 1.46 Da Aka Yi Watsi Da Shi A Kaduna
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna

November 8, 2025
Jerin Gwarazan Taurarinmu!
Rahotonni

Jerin Gwarazan Taurarinmu!

November 7, 2025
Next Post
bwari

Masarautar Bwari Jiya Da Yau

LABARAI MASU NASABA

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

November 14, 2025
NAHCON Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Kula Da Shafin Nusuk Masar Na Hajjin 2026

NAHCON Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Kula Da Shafin Nusuk Masar Na Hajjin 2026

November 14, 2025
NSCDC Ta Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Satar NAPEP Da Safarar Miyagun Kwayoyi A Kano

NSCDC Ta Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Satar NAPEP Da Safarar Miyagun Kwayoyi A Kano

November 14, 2025
Gwamnan Gombe Ya Gabatar Da Naira Biliyan 535.69 A Matsayin Kasafin 2026

Gwamnan Gombe Ya Gabatar Da Naira Biliyan 535.69 A Matsayin Kasafin 2026

November 14, 2025
Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba

Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba

November 14, 2025
Tinubu Ya Zuba Naira Tiriliyan 1.5 Don Bunkasa Noma Da Kayan Aiki Na Zamani

Tinubu Ya Zuba Naira Tiriliyan 1.5 Don Bunkasa Noma Da Kayan Aiki Na Zamani

November 14, 2025
Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko

Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko

November 14, 2025
Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima

Dalilin Asusun NADF Na Yin Hadaka Da Gwamnatin Jihar Jigawa

November 14, 2025
Xi Jinping Ya Gana Da Sarkin Thailand

Xi Jinping Ya Gana Da Sarkin Thailand

November 14, 2025
BUK Za Ta Kafa Cibiyar Horas da Aikin Jarida da Sabbin Kafofin Sadarwa Na Zamani

BUK Za Ta Kafa Cibiyar Horas da Aikin Jarida da Sabbin Kafofin Sadarwa Na Zamani

November 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.