Hukumar kididdiga ta kasar Sin NBS, ta ce darajar hajojin da masana’antun kasar Sin ke sarrafawa, ta karu da kaso 5.6 bisa dari a watan Afirilun da ya gabata.
Alkaluman adadin, wanda daya ne daga muhimman alkaluman auna bunkasar tattalin arzikin kasar, sun karu zuwa kaso 5.6 bisa dari a shekara, zuwa watan Afirilun da ya gabata. Kaza lika hukumar ta NBS ta ce karuwar ci gaban ta kai ta kaso 1.7 bisa dari sama da na watan Maris.
A daya hannun kuma, sashen masu tireda, dake sayar da hajojin bukatun yau da kullum na kasar, wanda shi ma muhimmin fanni ne na auna karfin sayayya a kasar, ya karu zuwa kaso 18.4 bisa dari a shekara guda a watan na Afirilu. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)