Duniya ta zura ido tana kallon yadda aka yi watanni ana zanga-zangar neman kifar da gwamnatin kasar Sri Lanka, inda a daidai ranar 13 ga watan Yuli shugaban kasar Gotabaya Rajapaksa ya tsere daga kasar kafin nan kuma Fitray Ministan kasar, Mahinda Rajapaksa, wanda dan uwa ne ga shugaban kasa ya yi murabus daga mulkin kasar.
Ginshikin rikicin ya samo asali ne saboda durkushewar tattalin arzikin kasar ne wanda hakan ya sanya gwamnatin ta kasa biyan basussukan da kasashen waje ke binta, an kuma fuskanci karancin makamashi da abinci, abin da ya kara harzuka al’umma shi ne yadda gwamnatin ta sanya dokar ta-baci ga al’ummar kasab a tare da la’akari da halin da suke ciki ba.
Amma yana da matukar sauki mutum ya fahinci yadda Sri Lanka ta fada cikin wadanna matsaloli na siyasa da tattalin arziki tun da ta samu ‘yancin kanta a shekarar 1948.
Babu mamaki a yadda aka fada matsalar tattalalin arziki. Bayan shekaru ana allubazaranci da tattalin arzikin kasa, gwamnatin Rajapaksa ta kuma ki neman tallafi daga Hukumar Lamuni ta Duniya IMF, wannan rashin daukar matakin ya sanya komai ya tabarbare a kasa, aka fada cikin wannan matsala a fannonin rayuwa gaba daya.
Tun daga gibi a kasafin kudin kasar da tsananin hauhawar farashi tare da rage darajar kudin kasa tare da dinbin bashin da ake bin kasa, dukkan alamu sun nuna an dunfari aukawa cikin rikici a sassan kasar.
Manyan kasashe da ke bin Sri Lanka bashi sun hada da Chana, Indiya da Japan inda Chana ke da kashi 10 da bashin da ake bin Sri Lanka gaba daya, irin wannan bashin da ta dabaibaibaye Sri Lanka ake yi wa lakabi da “Tarkon bashi na kasa da kasa.”
Al’umma kasar Sri Lankans sun mamaye titi don nuna bacin ransu a kan yadda tattalin arzkin kasar ya tabarbare, musamman matsalolin da suka hada da rashin wutar lantarki, rashin albarkatun man fetur, inda suka bukaci gwamnatin Rajapaksa ta gaggauta yin murabus, an fara zanga-zangar ne tun a watan Maris na wannan shekarar ta 2022.
Abin sha’awa anan shi ne yawancin masu zanga-zangar a cikin ‘yan Sri Lanka matasa ne daga kabilu daban-daban na kasar, duk kuwa da sojoji sun tatrwatsa masu zanga-zangar amma har yanzu makomar harkar siyasa da na tattalin arzikn kasar yana cikin kokwanto.
Tabbas rushewar Sri Lanka zai zama wata gaggarumar darasi wasu kasashe musamman wadanda ke fuskantar matsalolin tarin bashin kasa da kasa.
‘Yan Nijeriya na lura tare da kallon abin da ke faruwa na kasar Sri Lanka, muna kuma fatan shugabanin Nijeriya na lura da abin da ke faruwa a kasar. Tunanin cewa, irin wannan ba zai iya faruwa ba a kasar nan babbar kuskure ne.
Duk da wasu na iya nuni da cewa, akwai banbanci mai girma a tsakanin Nijeriya da Sri Lanka musamman abin da ya shafi yawan al’umma. Amma abin da ya kamata a lura da shi a nan shi ne lallai abubuwa basa tafiya yadda yakamata a kasar nan a halin yanzu.
A halin yanzu Nijeriya na fuskantar tsananin matsalar tattalin arzik da suka hada da rashin wutar lantarki, karancin man fetur da kuma tsawon lokacin da Malaman Jami’a ke yi a cikin yajin aikin da suka tsunduma da kuma uwa uba matsalar tsaro da ake fuskanta a sasan kasar nan. Duk da haka kuma lamarin almundahana da allubazaranci da kuma rashin gudanar da harkokin mulki na cigaba da gudana ba tare da tausayawa, wannan na tayar da hankali in aka lura da matsanancin halin da ake ciki a wannan lokacin.
Babban ginshikin tattalin arzikin kasar wanda shi ne Man fetur ya zama bashi da tasiri a kasuwannin duniya saboda kasashen duniya na kowawa amfani da wasu fasahar makashi don tafiyar da tattalin arzikinsu.
Wani abin lura kuma shi ne kusan shekara biyu ke nan da Nijeriya ta fuskanci gaggarumin zanga-zangar nan ta EndSars wanda aka yi makonni a na yi a manyan biranen kasar nan. Duk da cewa, zanga-zangar ya samo asali ne a kan tir da cin zarafin da ‘yansanda ke yi wa al’umma amma daga baya lamaran ya dauki sabon salo inda masu zanga-zangar ke bukatar tafiyar da harkokin gwwamnati yadda yakamata kafin daga baya aka yi zargin bata gari sun shiga cikin masu zanga-zangar inda aka fara tayar fa hankalin da barnata dukiyar al’umma.
Abin godiya a nan shi ne yadda masu zanga-zangar suka saurari kiraye-kirayen da aka yi musu na karkatar da korafinsu ta hanyar kada kuri’a wanda hakan ya kara zumudin matasan na shiga harkokin siyasa, amma har zuwa yasuhe ne wannan likimon zai cigaba?.
A kan haka babban aikin da ke a gaban masu ruwa da tsaki shi ne na tabbatar da an gudanar da sahihin zabe ba tare da magudi ba, duk wani abin da ya gaza haka zai iya haifar wa kasar nan matsalar da ba a san inda za ta iya kaiwa ba.
Kamar dai kasar Sri Lanka, Nijeriya ta fuskianci tarihin jam’iyyun siyasa na lashe zabe gaba daya tare da alkawurran da suke kasa cikawa ba.
Haka kuma kamar kasar Sri Lanka duk wanda ya zama shugaban Nijeriya a wannan karon dole ya jajirce ya kuma cika dukkan alkawurran da ya daukar wa al’umma, don kuwa a bayyana yake ‘yan Nijeriya ba za su bayar da uzuri ba a wannan karon.