Alhamadu lillah. Masu karatu assalamu alaikum wa rahmatullahi ta’ala wa barkatuh. Da fatan muna nan cikin koshin lafiya, Allah ya bai wa marasa lafiyarmu na gida asibiti koshin lafiya, ya kawo mana karin zaman kafiya a kasashenmu da duk duniya baki daya. Za mu kawo kashi na biyu na darussan da masu bibiya suka zakulo suka rubuto daga fahimtarsu game da zaman tafsirin da muka gabatar a Zawiyyarmu ta Ahlul Faidhati Mai Diwani Group da ke Kaduna, a watan azumin Ramadan da ya gabata.
-Kyawawan Dabi’u Ke Fayyace Tsoron Allah A Musulunci
Assalamu alaikum wa rahmtullah. Ya Sayyadi barkanmu da war haka, da fatan an yi sallah lafiya, Allah ya maimaita mana amin. Da farko muna mika godiya game da koyarwar da aka yi mana a zaman tafsirin bana wanda muka bibiya a kusan kullum, alhamdu lillah. Bayanan da kuka yi game da yadda littafan annabta da suka kunshi hukunce-hukunce da kuma alluna guda goman nan da Allah ya zabar ma Annabi Musa (AS) kuma suka zama hikima ga Annabi Isa (AS), sannan suka zama Furkanu ga Annabi Muhammad (SAW), sun nuna mana yadda Allah ya aiko annabawa a kan zuri guda na asali. Haka zalika, misalan da kuka bayar game da bambanci tsakanin takawar Musulunci (kyawawan dabi’u) da kuma takawar Imani (aiki gwargwadon iko) sun kara tabbatar mana da cewa duk wanda ya kasance mai tsoron Allah, za a same shi da kyawawan dabi’u.
A kan wannan gabar, ya kamata malamanmu su kara himma da yin kira ga al’ummar musulmi a kan mu muhimmanta yin adalci da kuma kyautata fahimta tsakanin mu musulmi da mabiyan sauran addinai. Kuma musamman su kansu Malamanmu na Musulunci ya kamata su guje ma saurin yanke hukunci ga al’umma, domin wanda ya kawo addinin, Manzon Allah (SAW) ya ce ya zo ne domin ya cika kyawawan dabi’u, don haka duk yawan karatun malami idan ba shi da kyawawan halaye to kuwa za a ga barna tana biyo baya. Hadisin da ka kawo na cewa, cikakken Musulmi shi ne wanda ‘yan’uwansa Musulmai suka kubuta daga cutarwar hannunsa da bakinsa, ya nuna mana cewa musulmi na kirki yana aikata tabbatattun abubuwa na ibadu kamar Sallah da Azumi amma kuma mu sani ba su ne kadai ba, dole a hada da kyawawan dabi’u kamar yadda muka gani daga Annabi (SAW). Allah ya ba mu ikon gyara halayenmu musamman ma a wannan zamanin. Jazakumullahu khairan
Sako daaga Salisu Usman Gombe
-Mun lura da ilimomin harkokin zamaninmu a cikin Alkur’ani
Cikin godiyar Allah, muna mika ziyara ga Shehu Isma’ila Umar Almadda (Mai Diwani) da kuma ban gajiya da gabatar da Tafsirin Alkur’ani mai girma na Azumin Ramadan na bana. Allah ya kai mu na badi albarkar Annabi (SAW) da Shehu (RTA).
Ya Shehi, a Tafsirinka na rana ta bakwai mun ji yadda ka yi bayani na ilimomin kiyaye hadurran hanya da ke kunshe a cikin aya ta 63 ta Suratul Furkan (Sura ta 25), “Wa Ibadur Rahman…”.
Mun kara fahimtar cewa, ayar tana nusarwa a kan tafiya cikin tsari walau sufuri ne na titin mota, ko na jirgin sama ko na ruwa ko jirgin kasa, da dukkan alamomin da ake sakawa na gane hanya da kiyaye aukuwar hadurra na ganganci da sauran ilimomin da suka kunshi dokokin hanya, duka suna nan a karkashin fahimtar ayar. Allah ya saka da alkhairi.
Game da sunan Allah na “Arrahmanu” kuwa, ya kara nuna mana cewa ya kunshi kowane ilimi. Kuma duk masana na sunan na “Arrahmanu” su ne suke zama kwararru na kowane fanni da ke tafiya a kan kasa cikin ilimi da kwarewa. Wallahi, wannan yana nuna mana cewa, mu al’umma musamman ta musulmi mu dage da neman ilimi na kowane fanni saboda inganta rayuwa da aiki da ilimin wajen nuna sanin ya kamata.
Daga misalan da ka kawo na batun hanya, na fahimci cewa, idan alamar hanya ta jar danja ta tsayar da direba shi kuma ya ki tsayawa, ya nuna jahilci ko rashin aiki da ilimin, wanda hakan ne yake sa jami’an da abin ya shafa suke hukunta direbobi masu karya dokokin hanya. Su kuma jami’an, yadda suke fara tambayar mai laifin a game da shin yana da lasisin tuki domin tantance cewa, shi a cikin “Ibadur Rahman” yake ko kuma jahili ne. Idan jahili ne hukuncinsa daban, idan kuma wanda ya san abin ne, watau yana daga cikin “Ibadur Rahman”, har yana da lasisi to hukuncinsa ma yakan fi tsanani, duka ya fahimtar da mu cewa muna da komai a cikin Alkur’ani.
Allah ya saka maka da alheri bisa yadda kuma ka karfafa gwiwar masu mulki har ma da magidanta a kan koyar da duk wadanda suke karkashinsu ilimi, domin tabbas jahilci tamkar mutuwa yake. Idan an ba mutane ilimi shi ne zai zama an raya su, haka nan idan an bar su da jahilci to kuma babu makawa an kashe su.
Muna godiya ya Shehi, Allah ya kara lafiya da nisan kwana.
-Tabbas Ya Kamata Mu Zurfafa Bincikenmu A Cikin Alkur’ani Domin Samun Ci Gaba
Assalamu alaikum. Ya Sayyadi barkanmu da kammala watan Azumin Ramadan, Allah ya amsa ibadunmu ya sa muna cikin ‘yantattun da aka ‘yantar, amin. Hakika bayanin da ka yi a kan yadda ya kamata mu al’ummar musulmi mu kara zurfafa bincike a cikin Alkur’ani domin samar da ci gaban zamani da ake gani a ko ina cikin duniya babban lamari ne mai matukar muhimmanci da ya kamata kasashenmu na musulmi mu mayar da hankali a kai.
Musamman ma, mu kasashen Afirka da muka zama koma baya idan aka kwatanta da sauran yankuna na duniya, ya kamata mu su sake nazarin wayewar zamani da ke kunshe cikin Alkur’ani, wanda hakan zai sanya mu iya yin kafada-da-kafada da manyan kasashen duniya irin su Amurka da China ta fannin ci gaban zamani.
Duk wanda ya san tarihi da kuma ilimi, ya san cewa duk bayanan da wadannan kasashen da suka ci gaba suke takama da su da kundayen da suka mallaka na bayanan ilimi muna nan da su a cikin Alkur’ani, abin da ya kamata a yi shi ne mu fadada bincike na fahimtar zamani a cikin Alkur’ani wanda hakan zai bai wa mu Afirka damar yin kirkire-kirkire da gudanar da sabbin ayyuka na ci gaban zamani.
Yana da kyau yadda muke da yawan mahaddata a Nijeriya, ya zama kasar ta zamo kan gaba wajen zama abar koyi a fannin kawo ci gaban zamani a Afirka da kuma inganta rayuwar ‘yan Afirka. Muna da yakinin cewa, in dai an sa hakan a gaba, tabbas nan da shekaru masu zuwa za mu iya cimma duk burin da muke so mu ga mun cimmawa.
Kuma har ila yau, mun ji dadi a kan kiran da ka yi na a sake nazarin wasu abubuwa na shari’a da ba su da asali a ainihin nassin da Allah ya saukar, domin tabbas abubuwan da Allah ya haramta da hukuncinsa (Muharramatu) kuma ya kulle su da hukunce-hukunce (Muhkamatu) babu wanda ya isa ya kara ko ya rage, kuma Allah bai bar su a dunkule ba, ya yi bayaninsu dalla-dalla.
Yadda aka fara shigo da abubuwa cikin addinin nan tun daga zamanin Sahabbai ya rikita abubuwa da yawa. Wannan ba rashin kunya ba ne ko kadan, muna girmama dukkan Sahabbai wallahi, kuma a cikinsu ne wasu suka tsawatar a kan shigo da abubuwa cikin addinin. Ga misalin Hadisin Ka’abu bin Malik, lokacin da wasu matasa suka ziyarce shi, suka yi masa kirarin girmamawa, suka bukaci ya yi musu hira daga cikin rayuwarsa tare da Annabi (SAW), wanda ya ce, musu “in kun ji na yi shiru ku ma ku yi shiru, yadda kaina ya yi fari (furfura) haka kwakwalwata ta yi, kuma abubuwa ne na yadda muka yi rayuwa da Rasulullahi (SAW). Bari na fada muku duk sai da aka canja su face Sallah (kadai), ita ma ga ta nan kun fara canzawa”. Duk wannan ya nuna cewa, ya kamata mu dawo kan turba ta asali.
Allah ya saka da alkhairi, ya Sayyadi. Wallahi muna godiya sosai, domin mun kuma karu da bayanai a kan abubuwan da Shari’a ke kewayawa a kansu na batun da ya shafi daukar kudi daga nan zuwa nan kamar rabon gado; da tsara Iyali da yadda za a yi aure da rabuwarsa da yadda za a yi tarayya a cikin dangi; da ukuba da hukunci a tsakanin abokan hulda. Haka nan, sauran harkoki irin su kokarin tabbatar da zaman lafiya wanda ya kunshi yadda ake shirya yaki, da sulhu, da zaman lumana; da batun riba da ke bayani a kan tsarin yadda za a gudanar da kasuwanci, sai kuma abubuwan da suka shafi dabi’o’i na ‘yan’adam.
Hakika duk sauran abubuwan da ba wadannan ba, Shari’a ta bar mutane su yi hukunci da abin da ke zamaninsu, na daga kundin tsarin mulki da ake shimfidawa don maslahar al’umma wajen habaka tattalin arziki da raya kasa.
Allah ya kara ilimi da fahimta a cikin wannan addini mai fadi da Manzon Rahama, Annabi (SAW) ya zo mana da shi domin tseratar da al’umma duka sai dai wanda ya ki. Mun gode.
Sako daga Malam Miftahu Adam Zariya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp