Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Kebbe/Tambuwal a Majalisar Wakilai, Honarabul Abdussamad Dasuki ya kaddamar da shirin tallafa wa mata da matasa masu kanana da matsakaitan sana’oi da manoma.
Shirin wanda aka yi wa taken “Yana Tafe” an kaddamar da shi ne ta hanyar bayar da cakin kudi kai tsaye ga wadanda suka amfana da manufar karfafawa sana’oinsu domin su kara zama masu dogaro da kai.
Honarabul Attahiru Umar Danmadi, mataimaki na musamman kan harkokin majalisa ga Honarabul Dasuki ne ya wakilci shi ya kuma bayyana cewar za su rika ziyartar kasuwanni da gonaki domin zakulo ‘yan kasuwa da manoma da suka fi bukata domin ba su cakin kudi domin karfafawa da habaka aikin noma, cinikayyar abinci da bunkasa kanana da matsakaitan sana’oi a mazabu 10 da ke a Kebbe da 11 da ke a Tambuwal.
Ya ce shirin wanda za a rika aiwatarwa a kowane wata daga gunduma zuwa gunduma, daya ne daga cikin alkawulan da Dasuki ya dauka a lokacin yekuwar neman zabe da zummar bunkasa tattalin arzikin al’ummar mazabar tare da kusanto da sha’anin wakilci kusa da al’umma ta hanyar sauke nauyin da suka dora masa.
“Mun assasa shiraruwa da dama na ayyukan raya mazaba da ci-gaban al’umma, a kwanan baya mun kaddamar da tallafin naira miliyan 100 wanda ya kunshi kudi, tallafin karatu da kayan abinci. A watan da ya gabata mun raba takin zamani ga manoma, yanzu kuma ga tallafin karfafawa manoma da masu kananan sana’o’i domin wadata al’umma da abinci da bunkasa sana’oi domin kara zama da kafafun su.”
A mabambantan tatttaunawarsu da LEADERSHIP Hausa, wasu daga cikin wadanda suka amfana, Maidamma Shekare, Mubarak Muhammad da Alhaji Hamisu Kuchi duka sun bayyana godiyarsu ga dan majalisar tare da alkawalin amfani da tallafin wajen inganta aikin gona da sana’o’in su.
A cewar su shirin zai taimaka kwarai ainun tare da yin tasiri a gare su manoma da masu matsakaita da kananan sana’o’i a yankunan karkara.