A daidai lokacin da makarantun firamare da sakandire da ke fadin kasar nan suka shiga sabon zangon karatu bayan dawowa daga hutu, galibin iyaye sun koka da karin kudin makaranta a yanayin kuncin rayuwa da ake ciki a halin yanzu, kamar yadda binciken LEADERSHIP ya nuna.
Wannan karin kudin ya zo daidai lokacin da ake samun raguwar kudaden shiga da zai dauki nauyin iyalai, saboda hauhawar farashin kayayyaki a fadin kasar nan sakamakon cire tallafin man fetur.
Iyayen daliban makarantun gaba da sakandare sun bayyana damuwarsu game da karin kudin makaranta a wasu jami’o’in Nijeriya. Wadannan jami’o’in, sun danganta karin kudaden na kashi 100 zuwa 200 bisa rashin isasshen tallafin kudi daga gwamnati da kuma hauhawar farashin kayayyaki.
Duk da kokarin da gwamnati ke yi na aiwatar da tallafin karatu ga daliban da ba su da galihu, mafi yawancin daliban ba su da tabbas game da makomarsu karatunsu.
Har ila yau, tashin hankali na kara karuwa a wasu jami’o’i, yayin da dalibai ke bayyana rashin jin dadinsu kan karin kudin makaranta da aka yi a baya-bayan nan, wanda ya haifar da zanga-zanga a fadin kasar nan. Misali, a kwanakin baya ne daliban Jami’ar Jos suka fito kan tituna domin nuna rashin amincewarsu da karin kudin makaranta da jami’a ta yi.
Masu zanga-zangan karkashin jagorancin kungiyar dalibai ta kasa, sun bukaci a gaggauta dawo da kudin makarantar yadda yake a baya. Masu zanga-zangan dauke da alluna masu dauke da sako kamar haka, “Idan yaranku za su iya biyan kudin, mu ba za mu iya ba” da “Ba ma son barin makaranta,” daliban sun bayyana kokensu.
Sun jaddada cewa tuni ‘yan Nijeriya suka fara kokawa da matsalolin tattalin arziki, kuma karin kudin makarantar zai kara ta’azzara lamarin. Zanga-zangar lumana da daliban suka gudanar ta haifar da cunkoson ababen hawa tare da toshe hanyoyin shiga harabar jami’ar.
Haka kuma, a jami’ar Legas (UNILAG), an samu ta tashin hankali a harabar jami’ar, yayin da kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta goyi bayan daliban na shirya zanga-zanga. Hasali ma, kwanan nan NANS ta ba da wa’adin sa’o’i 48 ga hukumomin jami’ar Legas da su sauya karin kudin makaranta.
NANS ta kuma yi kira ga daukacin manyan makarantu da ke fadin kasar nan su guji kara kudin makaranta, sannan ta yi gargadin cewa a shirye suke su hada kan mambobinsu a fadin kasar domin gudanar da zanga-zanga na rashin amincewarsu da irin wadannan karin kudin makaranta.
Ta bayyana wannan matsayar ne a yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a cibiyar ‘yan jarida ta kasa da kasa da ke Legas, biyo bayan dakile zanga-zangar lumana da ‘yansanda suka yi a UNILAG.
Kafin haka dai, NANS ta nuna rashin amincewarta da karin sama da kashi 300 na kudaden makaranta a jami’ar Ambrose Alli ta jihar Edo da ke Ekpoma. Daliban hadu a harabar kungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya (NUJ) na Jihar Edo, daliban sun bukaci a sake duba kudaden makarantar cikin gaggawa domin a samu zaman lafiya.
Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa tsadar rayuwa da tsadar kayayyakin aiki na kawo cikas ga ilimi, wanda hakan ya sa iyaye da dama ba su iya saka ‘ya’yansu a makaranta.
Makarantu masu zaman kansu sun kara wa daliban firamare da sakandire kudin makaranta sama da kashi 300, lamarin da ya kara haifar da fargabar cewa yawan daliban ba za su koma makaranta ba. Wasu iyaye na tunanin sanya ‘ya’yansu a makarantun gwamnati, yayin da wasu kuma ba su da tabbas kan matakin da za su dauka nan gaba, wanda haka zai kara haifar da karuwar yaran da ba sa zuwa makaranta.
Makarantu masu zaman kansu sun kara da cewa suna fuskantar tsadar kayayyakin koyo da kamarantarwa, wanda hakan ta sa dole ne su kara kudin makaranta.
Yayin da wasu malaman makarantu masu zaman kansu sun bayyana cewa suna fuskantar karancin albashi.