Dokar Lalalata Da Dalibai: Akwai Sauran Gibin Da Ba A Cike Ba

A dai-dai lokacin da Majalisar Dattawan Nijeriya ta gabatar da wata doka da za ta kai ga bai wa dalibai mata a manyan makarantu cikakken kariya daga nau’in zinace-zinace da keta musu haddi daga bangaren malamansu, al’umma musamman iyaye na ta sam-barka da maraba da wannan kyakkyawan yunkuri.

Wannan dokar da za ta dakile yawaitar cin zarafin mata ta nau’o’i daban-daban walau ko ta tursasa musu don basu maki ko wasu hanyoyin a manyan makarantun da suke kasar nan, ta zo ce  a lokacin da korafe-korafe kan yin lalata da daliban manyan makarantu ke kara ta’azzara.

Majalisar dattawan Nijeriya ta saurari kudurin a makon da ya gabata Laraba, kuma muddin kudurin ya zama doka, malamai za su iya shiga taitayinsu da taka-tsantsan wajen yin mu’amalar da ba ta dace ba da dalibansu musamman ma keta musu haddi.

To sai dai kuma, wasu na ganin har yanzu akwai sauran gibinda ya kamata majalisar ta cike a cikin dokar, kasancewar an tsara dokar babu wani tanadi na hukunta malaman addini masu lalata da mabiyansu ko dalibansu, wanda su ma ake samun yawaitar korafe-korafe na cin zarafin mata da keta wa yara mata haddinsu a wuraren ibada.

A daya barin ma, majalisar ba ta kalli cin zarafin da ake samu a makarantun sakandare da firamare ba, inda a wasu lokuta su ma akan samu makamancin wannan batutuwa na yin fyade wa yara kanana. Kodayake, majalisar bisa kudurin da aka gabatar ta yi fatan cewar za a karfafa bayar da shawarar a fadada dokar zuwa ga makarantun firamare da na sakandare.

A dokar da majalisar ta gabatar, an ware wa’adin shekaru har 14 ga dukkanin malamin babbar makaranta da aka cafke yana lalata da wata daliba a fadin kasar nan ba tare da wani zabi na biyu da ya wuce zaman gidan kaso na shekaru 14 ba.

Kudurin wanda ya zarce karatu na daya da na biyu a majalisar dattawan, mataimakin shugaban majalisar, Sanata Obie-Omo Agege shi ne ya gabatar da kudurin a gaban majalisar, da fatan kudurin idan ya zama doka zai kawo karshen cin zarafin mata.

A cewar shi; “Wasu masu bayar da shawara sun bayar da shawarar cewar a fadada wannan kudurin har zuwa makarantun Firamare da sakandari.

“Ba zan lamunci cin zarafi ko nenam yin lalata da dalibai a manyan makarantu ba; don haka dokar za ta kawo gyara da magance matsalolin da daliban mata suke fuskanta a manyan makaratun kasar nan ta fuskacin yin zina da su da lalata da su.

“Na gabatar da kudurin don ya zama doka ne domin bai dace a bar wannan fitsarar na ci gaba da yiyuwa ba, dokar za ta kawo kariya da tsaftace makarantu,” A fadin shi.

Ya ce samar da irin wannan dokar ya zama tilas lura da halin da ake ciki, “Kudurin ya shafi laifukan da suka hada da yin fyade wa dalibai ko tursasa musu yin lalata daga malamansu.

“Wannan dokar dai za ta sanya malamai su shiga taitayinsu gami kuma da tsarkake muhallan karatun dalibai daga barazanar fyade da cin zarafinsu,” in ji shi.

Sauran ababen da kudirin dokar hana fyaden ga dalibai matan ya kunsa sun hada da haramta rungumar dalibai mata, sumbantarsu, shafa su, taba su, taba musu kirji ko gashi, ko taba lebe ko kuma taba musu al’aura.

Haka kuma, ya kunshi haramta taba ko tayar da duk wata sha’awar jikin daliba, dukkan malamin da aka kama da hakan zai fuskanci hukuncin da aka tanada a kudirin, amma fa sai kudurin ya samu amincewa a majalisar ya zama doka.

Sanata Omo-Agege, ya bayyana cewar wadanan zafafan matakan ne za su kai ga kawo karshen matsalolin da ake ciki na cin zarafin dalibai a manyan makarantu.

Wani Dan Nijeriya mai nazari kan al’amuran yau da kullum, Alhaji Usman Isah ya yaba wa majalisar kan wannan kudurin, sai dai kuma ya ce akwai bukatar irin wannan dokar ga cibiyoyin addini wato a sanya takunkukumi ga malamai da fastoci domin su kansu ana samun makamancin hakan daga garesu.

“Ko a kwanakin baya an yi ta samu bayanai na wani fasto da ya yi lalata da wata a wajen ibada, don haka akwai bukatar malamai da fastoci su kansu a sanya musu irin wannan dokar domin tsaftace wuraren ibada da kuma bai wa mata kariya a kowani lokaci.

“Duk da ina fatan a samu ci gaba da tsaftace makarantu da kawar da cin zarafin mata, amma gaskiya akwai bukatar su kansu ‘yan matanmu su rika kula da irin shigar da suke yi wadanda ta hakan ne ke janyo hankalin maza zuwa garesu. “Ba ya ga wuraren ibada, akwai gayar bukatar a sanya dokar da ta fi irin wannan tsauri ma ga malaman firamare da sakandare domin dakile yawaitar keta wa yara kanana haddinsu a cikin kasar nan. Kowa ya san illar da lalata da kananan yara ke jawowa da jefa rayuwar yaran cikin gagari; don haka lokaci ya yi da za a samar da dokar mai tsauri domin kare mata a duk inda suke ba kawai manyan makarantu ba,” A fadin shi.

Dokar ta yi abar na’am ce ga kusan daukacin al’ummar kasa, sai dai matukar ana so komai ya tafi cikin tsari, ya kamata a fara tun daga tushe, a tabbatar da fadadata zuwa kananan makarantu da kuma cibiyoyin addini, domin nan din ma abubuwa suna kazanta da yawa a cikinsu

Exit mobile version