Wata ƙungiyar matasa mai suna “North-East Coalition Against Terrorism” ta yi maraba da Major General Abdulsalam Abubakar, sabon kwamandan yakin Operation HADIN KAI (OPHK), inda ta bayyana cewa tana fatan zaman lafiya ya dawo yankin.
A cikin wata sanarwa da Ismail Mustapha da Sakatare Danlami Bukar suka rattaba hannu, ƙungiyar ta ce Sojojin Nijeriya a ƙarƙashin babban Hafsan Soja Janar Chris Musa za su ci gaba da matsa lamba kan mayakan. Ta kuma yi kira ga al’ummar yankin su ba sabon kwamandan goyon baya.
- Boko Haram Sun Kashe Masu Kamun Kifi 18 A Borno
- Sojoji Sun Harbe Mutane Biyu Har Lahira Da Ake Zargi Ɓarayin Mota Ne A Filato
Ƙungiyar ta gargadi matasa su ƙi tayin shiga ƙungiyoyin da ba su da kyakkyawar manufa. Ta kuma bayyana cewa naɗin sabon kwamandan wani yunƙuri ne na ƙara sabbin dabarun yaƙi. “Ya daɗe yankin Arewa-Maso Gabas bai sami cikakkiyar zaman lafiya ba. Za mu ci gaba da zama a baya har sai dukkan al’umma sun goyi bayan Sojojin don shawo kan waɗanda suka jawo mana wannan rikicin,” in ji ƙungiyar North-East Coalition Against Terrorism
Ta kara da cewa; “Lokaci ya yi da za mu tattara mu goyi bayan Sojoji a ƙarƙashin Janar Chris Musa da sauran shugabannin Sojoji don dawo da zaman lafiya a yankinmu “
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp