Daga Bello Hamza, Abuja
An nemi al’ummar yankin Arewa su kawar da banbancin siyasa, kabilanci dana addini a tsakaninsu don fuskantar matsalar tsaro da kuma samar da matsaya guda daya don fuskantar harkar zaben 2023, ta hanyar fito da shugaba daya da zai nemi shugabancin kasar nan.
Shugaban kungiyar gamayyar kungiyoyin matasan yankin arewa maso gabas ‘Movement Of Northeast Youth Organization forum’, Alhaji Adburahaman Buba Kwacham ya bayyana haka a tattauanwarsa da manema labarai a garin Abuja ranar Alhamis. Ya kuma ce, yadda matsalar tsaro a yankin arewa ta ta’azarra a kullum kuma lamarin sai karuwa yake yi, har bamu natsu ba muka hada kai don samarwa kasar nan mafita ba, lamarin zai kai ga babu wata jiha da za ta kasance cikin zaman lafiya a cikin ta.
Alhaji Abdulraham Kwacham wanda yana cikin manyan ‘yan siyasa a Jihar Adamawa yana kuma shugabantar kungiyar gamayyar kungiyoyin matasan tun shekarar 1998, ya kuma nemi dukkan bangarorin siyasa a yankin Arewa su hada kai don tabbatar da mulki bai bar yankin ba a 2023, don a halin yanzu in har mulki ya kubuce daga arewa, ‘Bamu san yadda lamarin tsaro zai kasance ba, kuma zamu kara fuskantar gaggarumar koma baya a bangaren tattalin arziki da zamantakewa’ in ji shi.
Ya kuma yi kira na musamman ga al’ummar Arewa da su tabbatar da sun goyi bayan tsayyen dan siyasa daga yankin arewa kamar yadda suka yi a shekarar 2015 lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya fito takara, ‘’Talaka ya sadaukar da abin da ya mallaka ya tura wa kwamitin yakin neman zaben Buhari, suka kuma fito suka raka suka tsare har aka bayyana sakamakon zabe, irin wannan hadin kan ake bukata a halin yanzu don tabbatar da dan yankin arewa ne ya zama shugaban kasa a shekarar 2023’’ in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa, baya goyin bayan tsarin karba-karba, domin kuwa ba stari ba ne na dimokradiyya, “In har an samu mutanen da suka cancanta a cikin gida daya, ba laifi ne basu dammar mulki, haka kuma in har arewa keda mutanen da suka cancanta ai ba laifi bane” inji shi.
Daga karshe ya yi kira ga al’umma su jajirce su kuma shiga dukkan matakan siyasa da ake bukata don ta haka ne kawai za a iya samun nasarar tabbatar mulki a arewa, ya kuma yi addu’ar Allah ya zaba wa Nijeriya shugaba mafi alheri gare mu, Allah kuma ya bamu zaman lafiya.