Abdulrazaq Yahuza Jere">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Domin Karfafa Tsaron Iyaka, NIS Ta Kaddamar Da Sansaninta Na Belel

An Jinjina Wa Shugabancin Babandede A Taron

by Abdulrazaq Yahuza Jere
February 13, 2021
in LABARAI
2 min read
Domin Karfafa Tsaron Iyaka, NIS Ta Kaddamar Da Sansaninta Na Belel

Shugaban NIS Muhammad Babandede (a tsakiya) tare da sauran manyan bakin da suka halarci kaddamar da sansanin na Belel a Jihar Adamawa.

WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

A cigaba da kokarin da take yi na tabbatar da tsaro a kan iyakokin kasa da bakin-haure ke amfani da su, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta kaddamar da sansanin jami’anta na kan-iyaka a Belel da ke Jihar Adamawa.

Shugaban hukumar ta NIS, CGI Muhammad Babandede ya kaddamar da sansanin a ranar Juma’a 12 ga Fabarairun 2021.

samndaads

Kaddamar da sansanin na Belel ta sake nuna cewa Babandede da gaske yake yi a kan alwashin da ya dauka na tabbatar da karfafa tsaron iyakokin kasar nan, inda zuwa yanzu sansanin na Belel ya zama cikon na 15 da shugaban ya samar.

Da yake jawabi a wurin kaddamarwar, CGI Babandede ya gode wa manyan mutanen da suka halarci taron musamman wakilin Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri saboda goyon bayansa, da shugaban karamar hukumar Maiha Alhaji Idi Amin, da mai martaba Sarkin Mubi Alhaji Abubakar Isa Ahmadu, da Danburram Mubi Sarkin Belel, bisa kyakkyawar tarba da bayar da wurin masauki ga jami’an hukumar.

Sanarwar da ta fito daga Jami’in hulda da jama’a na NIS DCI Sunday James, ta yi bayanin cewa, shugaban karamar hukumar Maiha Alhaji Idi Amin ya yaba wa CGI Babandede saboda kyakkyawan shugabancinsa da hangen nesa wadda ta albarkarsu aka samu bunkasar ababen more rayuwa da kayan aiki a sassan hukumar da nufin kyautata jin dadi da yanayin aikin jami’ai.

Idi Amin wanda ya kasance tsohon jami’in NIS ya bayyana irin gagarumin sauyin da ya gani a sassan ayyukan NIS ga jama’a a cikin kankanen lokaci da hawa shugabancin Babandede, da nadinsa ya samu sambarka a ciki da wajen kasar nan.

 

 

SendShareTweetShare
Previous Post

‘Yan Jarida Sun Kauracewa Ayyukan Gwamnatin Jihar Sakkwato 

Next Post

Kafofin Watsa Labaran Birtaniya: Huawei Zai Kai Bankin HSBC Kara Domin Samun Muhimman Takardun Bankin

RelatedPosts

IITA Ta Fara Horas Da Matasa Sana`o`in Dogaro Da Kai A Zariya

IITA Ta Fara Horas Da Matasa Sana`o`in Dogaro Da Kai A Zariya

by Abdulrazaq Yahuza Jere
2 days ago
0

Daga Nasiru Adamu Cibiyar kula da albarkatun aikin gona ta...

Garkuwa Da Dalibai: An Ceto Daliban Kagara, Ana Cigaba Da Neman Na Jangebe

Garkuwa Da Dalibai: An Ceto Daliban Kagara, Ana Cigaba Da Neman Na Jangebe

by Abdulrazaq Yahuza Jere
2 days ago
0

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna Da sanyin safiyar asabar din...

Ma’aikatan Jinyar Jihar Ondo Za Su Fara Yajin Aikin Gargadi Na Kwana 3

Ma’aikatan Jinyar Jihar Ondo Za Su Fara Yajin Aikin Gargadi Na Kwana 3

by Abdulrazaq Yahuza Jere
2 days ago
0

Daga Idris Aliyu Daudawa kungiyar ma’aikatan jinya da unguwar-zoma ta...

Next Post
Kafofin Watsa Labaran Birtaniya: Huawei Zai Kai Bankin HSBC Kara Domin Samun Muhimman Takardun Bankin

Kafofin Watsa Labaran Birtaniya: Huawei Zai Kai Bankin HSBC Kara Domin Samun Muhimman Takardun Bankin

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version