Kwanan nan aka rufe taron kolin kungiyar tarayyar Afirka ta AU a kasar Habasha, inda wani muhimmin batun da shugabannin kasashen Afirka suka tattauna a kai shi ne rashin daidaito da adalci a duniyarmu.
Sabon shugaba na karba-karba na kungiyar AU, kana shugaban kasar Mauritania Mohamed Ghazouani ya ce, “halayyar tsarin kasa da kasa na yanzu ita ce rashin daidaito da wani ma’auni na bai daya, wadda ta kan haifar da matsala ga kasashe mafi raunin tattalin arizki.” A nasa bangare, Moussa Faki Mahamat, shugaban kwamitin kungiyar AU, shi ma ya ce, “batutuwa na rashin adalci na ta karuwa, kana matakan yin babakere, da neman daidaita rikici ta hanyar nuna karfin tuwo, sun zama ruwan dare. ”
- Ya Kamata Kasashen Yamma Su Ji Shawarwarin Kasar Sin Maimakon “Damuwa Da Asara”
- Kasar Sin Karfi Ce Ta Zaman Lafiya Da Daidaito A Duniya
Abokaina, na san kun taba ganin wasu abubuwa na rashin adalci. Misali, a lokacin barkewar annobar COVID-19, kasashen yamma sun yi kokarin ajiye dimbin alluran rigakafin cutar a gidajensu, matakin da ya mai da nahiyar Afirka “wata nahiyar da aka yi watsi da ita”, a fadin shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo.
Wani misali na daban da ya shaida yanayi na rashin adalci a duniya shi ne, yadda hauhawar darajar kudin dalar Amurka ta haifar da kwararar jari zuwa cikin kasuwannin kasar Amurka, lamarin da ya sa kasashen Afirka fuskantar matsala ta fuskar mayar da bashin dalar Amurka da ake binsu, gami da koma bayan tattalin arzikinsu, da kuncin zaman rayuwar jama’a.
Ban da haka, habakar kungiyar tsaro ta NATO zuwa gabas ta haddasa barkewar yaki tsakanin Ukraine da Rasha, sa’an nan dimbin makaman da ake bukata a fagen yaki sun sa kamfanonin kera makamai na kasar Amurka samun riba sosai, amma wannan yaki ya haifar da shinge ga kasashen Afirka a fannin samun hatsi da takin zamani daga kasashen Ukraine da Rasha, lamarin da ya sa karin jama’ar kasashen Afirka fadawa cikin mawuyacin hali, har ma da fuskantar yunwa.
To, shin me ya sa ake samun wannan yanayi na rashin adalci a duniya? Dalili shi ne, akwai dimbin abubuwa marasa dacewa cikin tsare-tsaren kula da al’amuran duniya da kasashen yamma suka gabatar. Kana tushen wannan matsala, shi ne yadda kasashen yamma suke yin babakere a duniya, a fannonin tattalin arziki, da siyasa, da aikin soja, gami da kimiyya da fasaha, da kuma yunkurinsu na kare wannan matsayi nasu na babakere har abada.
Ta yaya za a iya daidaita wannan matsala?
A cikin sakon taya murna da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aikewa taron koli na kungiyar AU na wannan karo, ya ambaci sauyawar yanayi da ake samu a duniyarmu, inda “Global South” (wasu kasashen da tattalin arzikinsu ke karuwa cikin sauri, da kasashe masu tasowa) da kasashen Afirka da kasar Sin ke wakilta, ke samun ci gaba, wanda ya haifar da babban tasiri kan al’amuran duniya. Wannan yanayi na hadin gwiwar kasashen “Global South”, da yadda suke kokarin raya kansu, a ganin Sinawa, abubuwa ne masu muhimmanci da za su tabbatar da kafuwar sabbin tsare-tsare masu adalci a duniya
Hakika muna iya ganin dimbin abubuwan dake faruwa, wadanda suka shaida hadin kan kasashen “Global South” da yadda suke yin tasiri a duniya.
Misali, bayan barkewar yaki tsakanin Rasha da Ukraine, kasashen yamma na neman shigar da kasashe masu tasowa cikin kasashe masu sanya wa kasar Rasha takunkumi. Amma kasashen “Global South” sun tsaya kan manufar diplomasiyya mai zaman kai, inda suka ki zama ‘yan amshin-shata na kasashen yamma, da magance fadawa cikin tarkon da aka dana musu, cewar wai akwai takarar da ake yi tsakanin rukunoni na dimokuradiyya da na mulkin kama karya.
Ban da haka, kasashe masu tasowa suna sa kaimi ga dunkulewar yankunansu waje guda don tabbatar da hadin kai da ci gabansu. Yanzu a nahiyar Asiya, ana kokarin aiwatar da shirye-shiryen hadin kan yanki, misali yadda ake gudanar da hadin gwiwar kasashe daban daban a karkashin laimar tsarin kungiyar hadin kai ta SCO, da tsarin hadin kan kungiyar ASEAN da kasashen Sin, da Koriya ta Kudu, da Japan. Kana bisa kokarin da kungiyar AU ta yi, an samu ci gaba sosai a nahiyar Afirka, a fannonin kwararar mutane tsakanin mabambantan kasashe cikin ‘yanci, da takaita shingayen harajin kwastam, da gina kayayyakin more rayuwa, da hanyoyin jigilar kayayyaki, da dai sauransu.
Sa’an nan, kasar Sin, bisa matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma, kuma daya daga cikin mambobin “Global South”, har kullum tana kokarin samar da gudunmowa ga ayyukan da za su kai ga samun ci gaba na bai daya na “Global South”.
A cewar Lalu Etalla, edita na gidan rediyon kasar Habasha, wanda ya halarci taron AU na wannan karo a wakilcin bangaren kafofin watsa labarai, bisa goyon bayan da kasar Sin ta bayar, an shigar da kasar Habasha cikin tsarin hadin gwiwa na BRICS, da mai da kungiyar AU daya daga cikin mambobin rukunin G20, duk a shekarar bara. Hakan ya kasance wata babbar nasarar da aka samu ta fuskar hadin gwiwar kasashen “Global South”.
Ban da haka, Marthe Boularangar, jami’a mai kula da aikin yaki da cin hanci da rashawa ta kungiyar AU, ta ce kasar Sin tana kokarin gina makarantu, da samar da kayayyaki da bayanai da ake bukata, a kasashen Afirka, gami da samar da kudin tallafin karatu ga daliban kasashen Afirka domin su yi karatu a kasar Sin don samun karin ilimi, ta yadda za a samar da dimbin kwararru masu ilimi, da taimakon kasashen Afirka wajen dogaro da kai a fannin tattalin arziki, da samun ci gaba mai dorewa. Hakan, a cewar Malama Boularangar, ya dace da babban jigon taron kolin kungiyar AU na bana, wato “Kafa wani nagartaccen tsarin ilimi a nahiyar Afirka”.
Cikin sakon da ya tura ma kungiyar AU, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya taya kungiyar murna kan yadda ta samu dimbin nasarori, a kokarinta na tabbatar da ganin hadin kan kasashen Afirka, da ci gabansu a fannoni daban daban. Saboda burin kasar Sin shi ne ganin hadin kai da ci gaban kasashe masu tasowa, wadanda za su tabbatar da sauyawar tsare-tsaren kasa da kasa zuwa masu adalci a nan gaba. (Bello Wang)