Hukumar tsaro ta DSS ta kama wani mutum da ake zargin ɗan bindiga ne, mai suna Sani Galadi, yayin da yake ƙoƙarin tafiya Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji.
An kama shi ne a ranar Litinin a Filin Jirgin Sama na Sultan Abubakar da ke Jihar Sakkwto, da misalin ƙarfe 11:15 na safe.
- NiDCOM Ta Ceto ‘Yan Nijeriya 13 Da Aka Yi Safarar Zuwa Ghana Da Mali
- Rasha Ta Ce Za Ta Tattauna Da Ukraine Don Yin Sulhu Game Da Yaƙin Da Suke Tafkawa
An cafke shi ne yayin ds ake tantance maniyyata.
Jami’an tsaro sun ce tun da farko suna sa ido a kansa kafin kama shi.
Wani babban jami’in tsaro ya tabbatar da kama shi.
Ya ce, “Eh, an kama Galadi yau yayin da ake tantance shi da nufin zuwa Saudiyya.”
Kama Galadi na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan kama wani riƙaƙƙen ɗan bindiga a sansanin alhazai da ke Abuja.
Ana zargin mutumin da hannu a wasu manyan sace-sacen mutane a Jihar Kogi da Abuja.
An shiga ruɗani yayin da wasu ke tambayar yadda mutanen da ake nema ke samun damar mallakar takardun tafiye-tafiye da wuce matakan tsaro ba tare da an gano su ba.
Amma jami’in DSS ya ce wannan tambaya ta shafi sauran hukumomi da ke bayar da fasfo da kula da tafiye-tafiye.
Ya ƙara da cewa, “Galadi yana hannunmu yanzu kuma yana amsa tambayoyi. Za a gurfanar da shi a kotu bayan an kammala bincike.”
ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa daga gwamnatin jihar ko wata hukumar tsaro game da kama Galadi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp