Dubun dubatan jama’a ne suka halarci sallar jana’izar marigayi Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi a ranar Juma’a.
An tsara gudanar da Sallar ne da ƙarfe goma na safiya kuma daidai wannan lokacin aka kabbara sallah.
- Fitaccen Malamin Musulunci Mai Da’awar Sunnah A Nijeriya, Dr. Idris Dutsen Tanshi Ya Rasu
- Duk Da Ayyana Nemansa Ruwa A Jallo, Dakta Idris Dutsen Tanshi Ya Dawo Bauchi
Wakilinmu da ya halarci jana’izar ya tabbatar da cewa dubban mutane ne suka halarci filin masallacin Idi da ke Games Village a cikin garin Bauchi domin sallar cikin jimami na rashi.
Wasu da muka zanta da su, sun nuna gayar jin zafin rashin malamin amma sun dangana komai ga Allah.
“Tabbas mun yi wa Malam shaida na gaskiya, adalci, rikon amana da gaya wa shugabanni gaskiya komai É—acinta. Muna jimamin rashinsa, amma mun yi imanin kowace rai za ta É—anÉ—ani mutuwa. Allah masa rahama,” inji Muhammad Adamu Gambo da ya halarci jana’izar.
“Malam bisa kyakkyawar mu’amalarsa duk da cewa ya kasance dodon yaki da Bidi’a ba zallar almajiransa ba ne suka halarci wannan jana’izar ka ga dai jama’a to ko’ina. Muna kyautata masa zato duk da an ce da kalmar shahada ya cika,” Aminu Sani, wani almajiransa.
Daga cikin wasiyoyin da Malamin ya yi sun haÉ—a da bai yarda da É—auke-É—auken hotuna wajen Janazarsa ba; babu zaman Makoki; ba turereniya wajen É—aukar gawarsa sannan kuma babu shiga makabarta da takalmi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp