Fiye da mutane 20 da ake zargi da safarar makamai da cefanen kayayyakin ga masu aikata laifuka aka kama su a ƙaramar hukumar Ifelodun da ke Jihar Kwara, a wani sumame da jami’an tsaro suka gudanar.
An gudanar da wannan kame ne bisa umarnin gwamnatin jihar da kuma Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan harkokin tusesaro, inda sama da jami’an tsaro na musamman 400 suka shiga aikin, wanda ya shafi ƙananan hukumomi irin su Ifelodun, Ekiti, Edu, Patigi da kuma wasu garuruwan kan iyaka.
Majiyar gwamnati ta bayyana cewa, “A yanzu haka, ana ci gaba da gudanar da bincike, kuma mutane sama da 20 sun shiga hannun jami’an tsaro. Wasu daga cikinsu an kama su da harsasai da kayayyakin da aka shirya kai wa masu laifi a yankin Babanla na Ifelodun.”
Majiyar ta ƙara da cewa, an tura mutum 10 daga cikin waɗanda aka kama zuwa Abuja tare da makaman da aka samu a hannunsu domin zurfafa bincike. Samamen ya kuma kai ga sakin fursunoni da dama da aka yi garkuwa da su a yankin saboda matsin lamba da ake yi wa ‘yan ta’addan.
Gwamnatin jihar ta yi kira ga al’umma da su kasance masu lura da kuma gaggauta sanar da hukumomin tsaro duk wani motsi da basu saba gani ba a yankin ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp