• English
  • Business News
Saturday, July 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Duk Dangi Suna Alfahari Da Samun Manzon Allah (SAW) A Cikinsu

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
2 years ago
in Dausayin Musulunci
0
Maulid
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Manzon Allah (SAW) yana da dangi da yawa, amma babu wadanda suka fi alfahari da shi kamar ‘ya’ya musamman wadanda suka fita daga jikinsa (SAW).

An tambayi Abdullahi bin Abbas (RA) shin mecece fassarar ayar da ta ce “ba na neman Lada daga gare ku, sai dai soyayya a cikin dangina?”, sai Sa’idu (wani malamin Kuraishawa) bin Jubairu bin Mud’amu bin Adiyyi ya yi sauri (kafin Abdullahi bin Abbas ya ba da amsa) ya ce “abin da ake nufi da dangi makusanta su ne iyalan gidan Annabi (SAW), sai Abdullahi bin Abbas ya ce ma sa “ka yi gaggawa, babu wani dangi na Kuraishawa face Manzon Allah (SAW) yana da kusanci da su, abin da ayar take nufi shi ne “sai dai ku sada abin da yake tsakanina da ku na zumunta.”

  • Tsoron Allah Da Ibadar Annabi (SAW)
  • Allah Ya Girmama Annabi (SAW) Cikin Fadi Da Aikatawa

Ibin Hajaral Askalani ya ce wannan fassara ta Sa’idu bin Jubairu ita ce wadda Aliyu bin Hussain (Zainul Abidiyn RA) yake kai, haka nan galibin malamai, ma’ana ana nufin a so iyalan gidan Manzon Allah (SAW).
Baya ga Aliyu Zainul Abidyn da ke kan wancan fassarar, Malamai irin su Saddi da Amru bin Shu’aibin duk sun tafi a kai kamar yadda Imamud Dabari ya fitar daga gare su.

Idan an dauki fassarar da Sayyidina Aliyu Zainul Abidiyn (RA) ya tafi a kai ne, to ayar tana kira ne ga dukkan duniyar musulmi su so dangin Annabi (SAW) makusanta. Idan kuma fassarar Sayyidina Abdullahi bin Abbas (RA) aka dauka, to magana ce ake yi da Kuraishawa wadanda Annabi (SAW) ya fito daga cikinsu, ma’anar “min anfusikum” na cikin “Lakad ja’akum”.

Idan kuma an dauki cewa ayar da Muminai take magana a matsayin makusanta, to ko wane Mumini ya shiga cikin makusantan Annabi (SAW), saboda Manzon Allah (SAW) ya ce wa Salmanul Farisi yana daga cikin iyalan gidansa. Don haka kowane Mumini shi ma yake alfahari da cewa daga cikinsu ne Manzon Allah ya fito.

Labarai Masu Nasaba

Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (2)

Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (3)

Da yake duk dangi suna alfahari da samun Manzon Allah (SAW) a cikinsu, mu ma a nan Afirka, Shehu Ibrahim Inyass (RA) ya ce muna alfahari da zamowar mu surukan Annabi (SAW) saboda ya yi sa-daka da Sayyida Mariyatul Kibdiya (‘Yar Misra daga kabilar Kibdayawa bakaken fata). Annabi (SAW) ya ce wa Sahabbai “idan kun bude Misra ku zauna mun da sirikaina lafiya”. Bayan Nana Khadija (RA) ta haifa wa Annabi (SAW) ‘ya’ya shida, babu wacce ta kuma haihuwa a cikin matansa masu girma da daraja sai Mariyatul Kibdiya wacce ta haifa masa Ibrahimul Mu’azzamu. Shehu Ibrahim (RA) ya ce wannan shi ne babban rabonmu, kenan muma muna da wani abu na kusanci da za mu yi alfahari da shi (SAW).

Haka nan Annabi (SAW) ya yi aure a cikin Yahudawa, don haka su ma za su yi alfahari da shi inda za su musulunta. Ya auri Sayyida Safiyyatu bintu Huyayyi bin Akhbar.

Wani abu na mata ya taba hada ta da Sayyida Aisha (RA) ta ce mata “Bayahudiya kawai”! Sai ta je da kuka ta fada wa Manzon Allah (SAW), sai Annabi (SAW) ya ce mata “A’a, ai ke kin wuce nan, ke ‘yar Annabi Musa ce ‘yar’uwan Annabi Haruna (AS).

Kowa zai yi alfahari da Annabi (SAW) kuma abin ya zamo ceto a gare mu ranar Alkiyama Albarkarsa (SAW).
Idan kuma muka koma bangaren wadanda suka tafi a kan “fataha”, a kan ayar Lakad ja’akum da muke bayani dangane da fassara ko ma’anar kalmar “min anfusikum” da ake karantawa da rufu’a ko “min anfasikum” da ake karantawa da fataha, kamar yadda aka samu daga wurin malamai. “Min anfasikum” ma’anar kalmar ita ce: Annabi (SAW) ya zo muku ne a matsayin mafi daukakar daraja a cikinku kuma mafificinku.
Karantawa da “rufu’a” ko “fatahar” duk yabo ne ga Annabi (SAW). Alkur’ani ya nuna Manzon Allah (SAW) mafificin kowa da kowa ne baki daya.

Bayan wannan kololuwar yabo da Allah ya yiwa Annabi, Allah ya kuma siffanta shi da kyawawan siffofi abin yabo da godewa da kirari masu yawa.

Allah (SWT) ya ce “Annabi (SAW) mai kwadayi ne a bisa shiriyar al’ummarsa (na shiga Musulunci da kara Imani a ciki), da nuna damuwa a kan duk abin da zai wahalar ya cutar da al’ummarsa a duniya da lahira, da nuna rahama da jinkansu (Muminai).

Wani sashe na Malamai sun ce Allah ya ba Annabi (SAW) wadansu sunaye guda biyu daga cikin nasa (SWT). Allah shi ne Ra’ufu (mai tausayi) kuma Rahimu (mai jinkai) amma sai ya ba Manzon Allah. Amma duk da haka, kyautar sunayen ba ta sa Manzon Allah ya zama Allah ba. Sunayen na Allah ne, shi kuma Annabi an bashi ne saboda girmansa a wurin Allah, ba nasa ba ne.

Kamar misali, wani Alhaji mai kudin gaske zai iya baiwa wani talaka rigarsa mai tsada ya sa, komai wuce wurin talakan nan ai don an bashi rigar Alhaji ya sa, ba zai shiga gidan Alhajin ya ce ya zama nasa ba saboda ya sa wannan rigar. Amma kuma samun rigar daraja ce sosai a wurin talakan.

Ba wadannan sunayen biyu ba kawai, akwai Malaman da suka kirga sunayen Allah guda 70 da Allah ya ba Annabi (SAW). Wasu Malaman kuma sun ce dukkan sunayen Allah guda 99 Allah ya ambaci Manzon Allah da su in ban da guda daya shi ne “Allahu”.

Haka nan, yana daga kirarin da Allah (SWT) ya yiwa Annabi (SAW) a cikin ayar nan ta Suratu Ali’imran, “Allah ya yi baiwa ga Muminai da ya aiko Annabi daga cikinsu…”. Da kuma wata aya ta Suratul Jumu’ah, “Allah shi ne ya aiko da Manzo a cikin Ummiyyai (Mutanen Makka ko Larabawa)…”. Da fadin Allah (SWT) a wata ayar, “Kamar yadda muka aiko da Babban Manzo a cikinku…”.

An karbo daga Sayyidina Aliyu bin Abi Dalib (Karramallahu waj’hahu) cewa, ma’anar fadin Allah (SWT) “Manzo ya zo daga cikinku” kamar yadda ya ji daga Annabi (SAW), ita ce “Annabi ya fi kowa dangi (babu dangi irin nasa), babu surukai irin nasa, babu iyaye irin nasa ko wanda yake da kwarewa irin tasa”, nasabarsa tun daga kan Annabi Adam (AS) har zuwa iyayensa (SAW) dukkansu aure ne suka yi babu zina”.

Malam ibn Khaldun ya ce ya kirga uwaye 500 a nasabar Annabi (SAW) har zuwa kan Annabi Adam (AS), amma ba a samu wadda zina ce ta yi ba aure ba kuma bai samu tarihin wani daga cikin iyayensa (SAW) sun aikata abin da jahilan lokutansu suka rika aikatawa ba.

An karbo daga Sayyidina Abdullahi bin Abbas (RA), ya ce ma’anar ayar “da jujjuyawar ka a cikin masu sujada” ita ce Allah ya fitar da tsatson Annabi (SAW) daga Annabi zuwa Annabi har shi ma ya fitar da shi Annabi. Ma’ana nasabar Annabi ba ta taba bi ta wurin wanda ba Annabi ba.

Shi a wurin Abdullahi bin Abbas (Farfesan Al’umma), duk iyaye da kakannin Annabi (SAW) Annabawa ne. Annabi shi ne wanda ake ma sa wahayi na shiriya amma ba a umurce shi ya isar ga kowa ba don ya shiryar da shi. Manzo kuma shi ne wanda aka saukar masa da shiriya sannan aka umurce shi ya isar ga wadanda aka aiko shi wurinsu.
Hakika da a yanzu ana bin irin wannan karatu da fahimta ta magabata na kwarai, masu fadar munanan kalamai a kan iyayen Annabi (SAW) ba za su yi ba. Domin Sahabin Annabi ne ya ce iyayensa (SAW) Annabawa ne.

Sayyidina Ja’afarus Sadik bin Muhammadul Bakir (Sharifi Jikan Annabi SAW) ya ce, “Allah ya san gajiyawar halittarsa wurin yi ma sa da’a, ya sanar da halittar don su san cewa su ba za su samu tsarki ba wurin bin sa amma ya tsayar da abin halitta (Manzon Allah) a tsakaninsa da su wanda za su gan shi, su iya koyi da shi (a harkokinsu na rayuwa) daga jinsinsu a wurin kama (‘Ya’yan Adam), sai Allah ya lulluba wa Annabi (SAW) sifarsa ta jintausayi da jinkai (Kamar yadda ya kira Manzon Allah da Ra’ufu da Rahimu), sannan ya fitar da shi zuwa ga halitta a matsayin wakilinsa mai gaskiya, ya sanya bin shi (Annabi) a matsayin bin sa (Allah), dacewa da abin da ya zo da shi; dacewa ne da abin Allah”.

Allah Ta’ala ya ce “duk wanda ya bi wannan Manzon, ya bi Allah ne”. Allah Ta’ala ya ce “ba mu aiko ka ba face kai rahama ne ga dukkan talikai.”

Malam Abubakar Shadibi ya ce “Allah ya kawata Annabi Muhammad (SAW) da ado na jinkai, sai shi kansa ya zamo Rahama, duk dabi’o’insa Rahama ne, siffarsa ma Rahama ce ga halitta, duk wanda wani Abu ya same shi daga wannan Rahama ta Annabi (SAW) ya tsira duniya da lahira daga dukkan abin ki. Duk wanda ya sadu da dabi’o’in nan na Manzon Allah abin so ne dukkansa. Shin ba ka gani ba Allah yana cewa “ba mu aiko ka ba face kai jinkai ne ga al’umma”. Sai rayuwar Manzon Allah (SAW) ta zamo Rahama, komawarsa ga Allah ma ta zamo Rahama Kamar yadda ya fada cewa “rayuwata alheri ce gare ku, rasuwata ma alheri ce gare ku”. Da kuma yadda Manzon Allah (SAW) ya ce “idan Allah ya so Rahama ga al’umma sai ya karbi ran Annabinta kafin al’ummar; sai ya sanya shi marigayi ko magabaci mai gyara gare ta (wanda zai shirya ma al’ummar komai a wurin Allah).


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Annabi SAWShehu Ibrahim InyasTsoron Allah
ShareTweetSendShare
Previous Post

Kamfanonin Jirage Za Su Fara Biyan Tarar Jinkirta Tashi Da Soke Tafiya

Next Post

Wani Mutum Ya Halaka Kansa A Jihar Adamawa

Related

Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (2)
Dausayin Musulunci

Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (2)

16 hours ago
Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (3)
Dausayin Musulunci

Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (3)

2 weeks ago
Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (1)
Dausayin Musulunci

Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (1)

3 weeks ago
Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (3)
Dausayin Musulunci

Darussan Hadisin Aikin Hajjin Manzon Allah S.A.W (2)

4 weeks ago
Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (3)
Dausayin Musulunci

Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (3)

1 month ago
Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (1)
Dausayin Musulunci

Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (1)

2 months ago
Next Post
Wani Mutum Ya Halaka Kansa A Jihar Adamawa

Wani Mutum Ya Halaka Kansa A Jihar Adamawa

LABARAI MASU NASABA

Nazari Kan Taraktoci 2,000 Da Tinubu Ya Kaddamar Don Bunkasa Noma

Nazari Kan Taraktoci 2,000 Da Tinubu Ya Kaddamar Don Bunkasa Noma

July 12, 2025
Kashim Shettima Ya Mayar Da Martani Kan Tsadar Rayuwa

Rashin Ganin Shugabannin APC Yayin Ziyarar Shettima A Kano Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara

July 12, 2025
Sin Na Goyon Bayan G20 Ta Ci Gaba Da Ba Da Kyakkyawar Gudummawa

Sin Na Goyon Bayan G20 Ta Ci Gaba Da Ba Da Kyakkyawar Gudummawa

July 11, 2025
Hadakar Jam’iyyar ADC Ta Fara Dusashe Karfin PDP A Wasu Jihohin Nijeriya

Hadakar Jam’iyyar ADC Ta Fara Dusashe Karfin PDP A Wasu Jihohin Nijeriya

July 11, 2025
Kasar Sin Na Da Muradin Zurfafa Hadin Gwiwar BRI Da Masar 

Kasar Sin Na Da Muradin Zurfafa Hadin Gwiwar BRI Da Masar 

July 11, 2025
Nijeriya Na Fuskantar Siyasa Mara Tabbas —  Peter Obi

2027: Takarar Shugaban Kasa Zan Yi Ba Mataimaki Ba – Peter Obi

July 11, 2025
“Sin Daya Tak A Duniya”, Matsaya Ce Da Al’ummun Duniya Suka Kafe Kai Da Fata a Kai

“Sin Daya Tak A Duniya”, Matsaya Ce Da Al’ummun Duniya Suka Kafe Kai Da Fata a Kai

July 11, 2025
2027: Masu Ruwa Da Tsaki Sun Bukaci A Kawo Karshen Matsalar Sayen Kuri’a

2027: Masu Ruwa Da Tsaki Sun Bukaci A Kawo Karshen Matsalar Sayen Kuri’a

July 11, 2025
Wang Yi Ya Gana Da Sakataren Harkokin Wajen Amurka

Wang Yi Ya Gana Da Sakataren Harkokin Wajen Amurka

July 11, 2025
Fahimtar Kyawun Bambance-Bambance Kyakkawar Hanya Ce Ta Wanzar Da Zaman Jituwa A Duniya

Fahimtar Kyawun Bambance-Bambance Kyakkawar Hanya Ce Ta Wanzar Da Zaman Jituwa A Duniya

July 11, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.