Tsohon Gwamnan Jihar Neja, Dakta Mu’azu Babangida Aliyu ya bayyana cewar duk Gwamnan da ya gaji ko ya kosa da tabarbarewar sha’anin tsaro a Jiharsa, ya sauka ya koma kauyen su.
Talban na Minna ya bayyana hakan ne a jiya a yayin da yake gabatar da kasida mai taken “Matsayin Kwalejin Ilimi Ga Ci-gaban Nijeriya” a bukin cika shekaru 50 da kafuwar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sakkwato.
“Ina mamaki idan na ga kanun labarai cewar Gwamnoni sun gaji da rashin tsaro. Babu Gwamnan da ya kamata ya damu ko ya gaji da rashin tsaro, idan kuma har ya yi haka to ya yi murabus ya koma kauyen su.” Ya bayyana.
“Shugaban Karamar Hukuma yana da aikin yi kuma mafi yawan Gwamnoni ba su girmama Sarakunan gargajiya bayan kuma su ne suke da gogewa. Ya zama wajibi Gwamnoni su yi amfani da Hukumomin da ke karkashin su, su yi aikin su, domin babban aikin su shine tabbatar da tsaron rayukan al’umma da dukiyoyinsu. Don haka idan na ga kanun labarai ina girgiza matuka.”
Aliyu wanda tsohon dalibin kwalejin ne ya bayyana cewar ya baiwa jami’an tsaro cikakken yanayin aiki tare da kula da jin dadi da walwalar su yadda ya kamata. “Abin da nake fada shine idan aka turo jami’an soji a Jihar Neja, an turo ka ne ka taimaka mani ba wai ka kasheni ba. Ban nuna masu kabilanci ba, dukkanin su mun dauke su a matsayin ‘yan Jiha.”
“Duk lokacin da aka samu matsalar tsaro ba mu jiran Gwamnatin Tarayya ta turo kudi, idan har muka jira to duk za mu mutu, don haka muke daukar matakin gaggawa domin shawo kan matsalar.”
Da yake magana kan ta’addanci, ya bayyana cewar “Akwai jita-jitar cewar an gayyato ‘yan ta’adda domin su yaqi Gwamnatin Jonathan. Ko hakan gaskiya ne ko akasinsa ba ya da amfani a yanzu. A yanzu hatta Fulanin mu sun jikkata sosai, an sace shanunsu, sun kuma fara daukar fansa.”
Tsohon Gwamnan wanda ya bayyana muhimmanci da tasiri ilimi ya fi gaban a nanata, ya yi wa kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU bulala da cewar ya kamata su kasance a matsayinsu na kungiyar kwararru maimakon ta kasuwanci.