Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta ƙaddamar da wata runduna mai dakaru 5,000 domin yaƙi da ta’addanci da sauran laifuka a yankin.
Ministan Tsaron Nijeriya, Mohammed Badaru Abubakar, ne ya bayyana haka a taron hafsoshin tsaro karo na 43 da aka gudanar a Abuja.
- Gwamna Buni Ya Naɗa Matasa 200 A Matsayin Hadimansa
- Cutar Sanƙarau Ta Kashe Mutum 26, 248 Sun Kamu A Kebbi
Taron ya samu halartar manyan hafsoshin tsaro daga ƙasashen ECOWAS, ban da Mali, Burkina Faso da Nijar, waɗanda suka fice daga ƙungiyar a hukumance a ranar 29 ga Janairu, 2025.
A cewar Badaru, kafa wannan runduna yana da nufin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin, tare da amfani da kwarewa, kayan aiki, da sadaukarwa domin cimma nasara.
“Ina mai farin cikin sanar da fara aikin wannan runduna domin yaƙi da ta’addanci a yankin,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, ECOWAS na da aniyar tunkarar matsalolin tsaro don tabbatar da zaman lafiya da wadata ga al’ummomin ƙasashen yankin.