Shugabannin kungiyar ECOWAS sun sake shimfida wasu ka’idoji da suka ce ya zama dole sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar su bi matukar suna bukatar kungiyar ta janye takunkumin da ta kakaba wa kasar.
Cikin ka’idojin har da bukatar ganin sojojin sun dauki hanyar mika mulki a hannu farar hula.
- Kyautar CAF ta 2023: Super Falcons Ta Lashe Kyautar Tawagar Mata Mafi Kwazo A Afirka.
- Fitacciyar ‘Yar Jarida, Aisha Bello Mustapha Ta Rasu
Shugabannin na wadannan kalamai ne cikin matsayar da suka cimma a taron da suka gudanar kan halin da ake ciki a kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso, a Abuja.
Shugaban majalisar kungiyar ta ECOWAS, Omar Touray ya ce tawaga daga kasashen Benin, Togo da kuma Saliyo za su sake bude wani zauren tattaunawa da gwamnatin sojin Nijar don duba yiwuwar cimma matsaya game da mika mulki a hannun farar hula.
Touray, ya ce ECOWAS za ta dauki matakin janye takunkumin ko kuma barin sa ne bayan nazartar rahoton da tawagar za ta gabatar bayan kamalla ganawa da gwamnatin sojin Nijar.
“Abin da kadai zamu saurara don janye wa Nijar wadannan takunkumai su ne sojojin su bai wa gwamnatin rikon kwarya damar karbar mulki matukar ba haka ba kuma za mu ci gaba da sanya wa kasar sabbin taukunkumai,” in ji Touray.
Jerin takunkuman da ECOWAS ta kakaba wa Jamhuriyar Nijar ya jefa jama’ar kasar cikin kunci, yunwa, rashin kudade da kuma ta’azzarar matsalar tsaro.