Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta ce ta ceto jimillar mutane 31 da aka yi garkuwa da su a wani samame na hadin gwiwa a Jihohin Edo da Taraba, biyo bayan musayar wuta da wasu da ake zargin makiyaya ne.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Muyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, inda ya bayyana nasarorin da aka samu a matsayin karin shaida na jajircewar rundunar na kare rayuka da kuma tabbatar da tsaron kasa.
- NSCDC Ta Gurfanar Da Wanda Ake Zargi Da Badakalar Naira Miliyan 159
- Gwamna Yusuf Ya Kafa Kwamitin Bincikar Kwamishinan Sufuri Kan Karɓar Belin Dilan Ƙwaya A Kano
A cewar Adejobi, a Jihar Edo a ranar Juma’a, 11 ga watan Yuli, 2025, da misalin karfe 7:20 na rana, jami’an rundunar ‘yansandan jihar sun mayar da martani ga wani mumunar garkuwa da mutane da aka yi a hanyar Fugar-Agenebode a Karamar Hukumar Etsako ta Gabas. Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi wa matafiya kwanton bauna, inda suka kashe biyu tare da yin awon gaba da wasu da dama.
Wani aikin hadin gwiwa da jami’an ‘yansanda da jami’an tsaron yankin suka yi cikin gaggawa ya kai ga gudanar da aikin ceto a yankin tsaunin Obe da ke kusa da layin Ajaokuta. An yi artabu tsakanin jami’an ceto da masu garkuwa da mutane, lamarin da ya tilasta wa masu laifin tserewa da raunukan harbin bindiga. An yi nasarar kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su goma sha hudu a yayin aikin.
Sanarwar ta kara da cewa, “A Edo, tawagar ceto ta yi artabu da masu garkuwa da mutane a wani fadan bindiga a kusa da tsaunin Obe, inda suka gudu da raunuka daban-daban. Ya kara da cewa ana ci gaba da kokarin cafke wadanda ake zargi da guduwa.
A wani lamari makamancin haka da ya faru a Jihar Taraba, a watan Yuli, 2025, da misalin karfe 11:45 na rana, jami’an ‘yansanda sun amsa kiran da aka yi musu na satar mutane a hanyar Wukari, jim kadan a bayan jami’ar tarayya ta Wukari. Wata farar mota kirar Toyota bas dauke da fasinjoji 17 daga Enugu zuwa Yola, wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi musu kwanton bauna.
Jami’an ‘yansanda tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro sun yi gaggawar kai farmaki inda lamarin ya faru. Da ganin tawagar jami’an tsaro na zuwa, sai masu garkuwar suka yi bar wadanda abin ya shafa suka gudu cikin daji. An ceto dukkan fasinjoji 17 ba tare da jin rauni ba.
Sufeto-Janar na ‘yansanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya yaba da yadda jami’an ‘yansanda suka yi gaggawar daukar matakin. Ya sake nanata cewa rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ci gaba da jajircewa a kokarinta na wargaza hanyoyin sadarwar masu laifi a fadin kasar.
“Wadannan sakamakon da aka samu sun nuna irin kwarin gwiwar da rundunar ‘yansandan Nijeriya ta yi na kare lafiyar ‘yan kasa da kuma tsaron kasa,” in ji IGP, yana mai ba da tabbacin cewa za a ci gaba da gudanar da ayyukan da aka yi niyya tare da sabunta kwarin gwiwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp