Hukumar Yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC ta bayyana wani ɗan kasuwa kuma surukin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, Abdullahi Bashir Haske, a matsayin wanda ake nema bisa zargin haɗin baki da halatta kuɗi ta barauniyar hanya.
A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Dele Oyewale, ya fitar a shafukan sada zumunta na EFCC a daren Alhamis, hukumar ta bukaci jama’a da duk wanda ke da sahihan bayanai game da inda Haske yake, da ya kai rahoto zuwa ofishin ƴansanda mafi kusa ko kuma zuwa dukkanin ofisoshin EFCC a faɗin ƙasa.
- EFCC Ta Kama Daraktocin NAHCON 2 Kan Zargin Karkatar Da Kuɗin Hajjin 2025
- NGF Ta Yi Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifin Gwamna Ododo
Mai shekaru 38, wanda aka kuma wallafa hotonsa, ana neman sa bisa laifin haɗin baki da kuma zargin halatta kuɗin haram. An bayyana gidajen da ya fi zama a baya a matsayin lamba 6, titin Mosley, Ikoyi, Lagos, da kuma lamba 952/953, titin Idejo, Victoria Island a jihar Legas.
Hukumar ta roƙi ƴan Nijeriya da su ba da haɗin kai wajen gano inda yake ta hanyar kai sahihan bayanai ga ofisoshin ta da ke Ibadan, Uyo, Sokoto, Maiduguri, Benin, Makurdi, Kaduna, Ilorin, Enugu, Kano, Lagos, Gombe, Port Harcourt, da Abuja. Haka kuma ta bayyana cewa za a iya tuntuɓar hukumar ta wayar tarho ko kuma ta adireshin imel ɗinta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp