Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), ta kama wasu mutum 17 da ake zargi da damfara a Intanet a Makurdi, babban birnin Jihar Benue.
A wata sanarwa da shugaban hukumar EFCC na jihar, Wilson Uwujaren, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce an kama su ne biyo bayan bayanan sirri da aka samu.
- Gobara Ta Tashi A Wani Kamfani Da Ke Jihar Legas
- Shugaban Jam’iyyar NNPP Na Kasa, Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa
Wadanda ake zargin dai sun hada da Emmanuel Victor, Joseph Adoyr Ameh, Olamide Timothy, Augestine Adalache, Izuka Justin, Boniface Dudoo, Udechukwu Benedict, Emmanuel Igbo.
Sauran sun hada da Emmanuel Ikechukwu, Agbo Lawrence, Favor Nwokdi, Christian Nwgia, George Maaki, Yina Terseem, Wilson Egwoba, Isaac Ukange da Precious Tseaa.
Kayayyakin da jami’an EFCC suka kwato sun hada da wayoyin hannu, katin ATM, kwamfuta, mota kirar Lexus RX330 da kuma mota kirar Toyota Camry.
Uwujaren ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun yi maganganu masu amfani kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su gaban kotu.